KOKARIN BALLEWAR IPOB DAGA NAJERIYA: Nnamdi Kanu zai kashe naira miliyan 300 wajen neman goyon bayan Amurka

Shugaban haramtacciyar Kungiyar IPOB, mai rajin ballewa daga Najeriya don su kafa Jamburiyar Biafra wadda ta kunshi Jihohin kabilar Igbo gurguzun su, zai kashe naira miliyan 300 wajen neman biyan bukatar samun goyon baya da amincewar Amurka.

Kano ya rattaba takardar yarjejeniyar kashe dala 750,000, kwatankwacin naira miliyan 300 wajen biyan wasu kwararrun sojojin bakan Amurka, (lobbyists), wadanda za su rika yi wa IPOB ‘jagaliyancin’ da Amurka za ta gamsu da manufofin IPOB.

Wannan yarjejeniya za ta kai ga Kanu ya biya wadannan ‘yan jagaliya naira miliyan 300 a cikin watanni 12.

PREMIUM TIMES ta ga gilmawar kwafe-kwafen yarjejeniyar, kuma ta yi nasarar damke su a hannun ta.

Kanu ya sa hannun yarjejeniyar da wani kamfanin kwararrun ‘yan jagaliya mai suna BW Global Group (BWGG), LLC, na Amurka, tun a cikin watan Fabrairu.

Kamfanin dai wani mai suna Jeffrey Birrel da Alan White ke da shi, kuma su ne su ka yi masa rajista a birnin Washington D.C na Amurka.

Ana sa ran kamfanin zai rika bibiyar manyan jami’an gwamnatin Amurka, ‘yan majalisar dattawa, hukumomin tsaro da ofishin Harkokin Kasashen Waje na Amirka da manyan ‘yan siyasa da masu fadar ra’ayoyin su a ji, su na tallata masu alfanun kafa Biafra.

Wannan yarjejeniya dai ta fara aiki tun a ranar 1 Ga Maris, 2021.