Iran ta gamu da gudumar Ingila a Qatar, ta jibga mata kwallaye 6 da raga

A wasa ta biyu da aka buga a kasar Qatar n a cigaba da wasan ƙwallon kafa na cin kofin Duniyq da aka buga ranar Litini, kasar Iran bata saha da daɗi ba a hannu Ingila.
Tun daga farkon rabin lokaci Ingila ta fara dirka wa Iran kwallaye a raga babu sani ba sabo.
Kafa n karshe wasa kuwa, Ingila ta zura wa Iran kwallaye har 6 a raga.
Sai dai maimakon abin kunyar ya yi yawa Iran ta samu ta jefa kwallo biyu kafin a tashi wasa
An tashi wasa 6-2.
Dan wasan Arsenal Saka ya jefa Kwallaye biyu a ragar Iran kafin aka canja dhi da Rashford na Manchester United. Shima kuma yana shiga ya jefa ta sa kwallon.
Grealeash na Manchester City shima ya jefa kwallo daya a wasan.
A wasan ranar farko, wato ranar Lahadi, Equador ta lallasa mai masaukin baki da ci 2-0.