Yadda QATAR 2022 ya bambanta da saura gasannin baya

Ya kamata mai karatu ya san cewa Qatar ta kashe Dala biliyan 220 cikin shekaru 12 wajen yin shirye-shiryen da su ka haɗa da gina filayen wasanni takwas, manyan titina, gadoji, otal-otal da sauran su.

Ba a taɓa yin kashe kuɗi wajen ɗaukar nauyin Cin Kofin Duniya a baya kamar yadda Qatar ta kashe. Ko rabin na ta ma wata ƙasa ba ta taɓa kashewa ba.

An haramta shan barasa, shigar banza, sumbanta da nuna alamomin goyon bayan ‘yan luwaɗi, maɗigo, masu sauya jinsin halitta da dukkan nau’ukan alfasha a sitadiyan.

Wani danƙareren jirgin ruwan yawon shaƙayawa ya isa bakin gaɓar ruwan Qatar.

Jirgin ruwan zai riƙa yawo da fasinjoji masu son yawon buɗe ido. Ya na da ɗakunan 2733, kuma ya na ɗaukar fasinjoji sama da guda 6,000.

Abin birgewa dukkan filayen wasan takwas an bi wurin zaman ‘yan kallo an sa rinɗima-rinɗiman na’urorin sanyaya jiki da busa iska, maganin tsananin ranar da ake yi a Qatar.

Wannan ne karo na farko da wata ƙasar Larabawa ta ɗauki nauyin shirya gasar Cin Kofin Duniya. Kuma ita ce ƙasar da ta fara shan kashi a tarihin wasan ƙwallon ƙafa tun bayan fara gasar cikin 1930.

An shafe shekaru ana gina ƙasaitattun ayyukan da su ka bunƙasa ƙasar cikin shekaru 12.

Cikin waɗanda su ka halarci buɗe gasar, har da Babban Basaraken Dubai, Sheikh Mohammed Rashid al-Maktom, Shugaban Masar Abdul Fatah al-Sisi da Sarkin Saudiyya, Mohammed bin Salman.

Yayin da Qatar ce ƙasa mafi ƙanƙantar da ta taɓa ɗaukar nauyin Gasar Cin Ƙofin Duniya, an tabbatar da ba a taɓa shirya ƙasaitacciyar gasar kamar ta Qatar ba.

Amurka, Mexico da Canada ne za su yi haɗin gwiwar ɗaukar nauyin gasar ta shekarar 2026, nan da shekaru huɗu masu zuwa.