Ina Mamakin Yadda ‘Wani Lokacin’ Muke Tozarta Iyayen Mu Da Sunan Murna – Bashir Kano

Akwai bambanci tsakanin yin biyayya ga iyaye fa, da kuma kare masu mutuncin su; ko nuna martaba da ƙimar su a idanun Duniya.

Haƙiƙa, wajibi ne a gare mu; mu yiwa iyayen mu biyayya – kuma mu girmama su. Wannan batun kowannen mu ya san shi, ba sai an fada ba.

Ban sani ba, ko wani lokacin muna kasa fahimtar dabi’un guda biyu ne. Ko, wani lokacin muna daukar su a matsayin Abu guda.

Misali, duk biyayyar da muke yiwa iyayen mu – amma a waje muna aikata ba dai-dai ba, to lallai ba ma yin abinda zai tabbatar da ƙimar su a idanun Duniya.

Su iyaye, ko mun girma; muna buƙatar aikata abin ƙwarai – domin zai riƙa tunatar da jama’a irin ƙoƙarin da suka yi akan mu wajen ba mu tarbiya; har ‘wataƙila’ ma suyi masu addu’a.

Wani lokacin, sauka daga kan hanyar da iyaye suka dora namiji, yakan zama da sauƙi-sauƙin tuhuma, ko zubar da mutuncin iyaye fiye da mace – wacce har ta mutu idan dabi’un ta munana ne, za’a riƙa yiwa iyayen ta kallon wadanda suka gaza.

Shine yasa, idan mace ba ta da halayen ƙwarai sai mutane su riƙa cewa “ai duk iskancin da ‘wacce’ za tayi; ba za ta kama ƙafar tshohon ta ‘wane’ ba” – domin su nuna cewa bai ba ta tarbiyya ba.

Amma namiji, dama shine tsayayye; kuma jigon iyali. Akwai shekarun da idan ya cimma masu, duk abinda zai aikata – shi a karan kan sa mutane za zarga; sabida ‘wataƙila’ shima ya tunkari hanyar zama uba; ko wanda ya kamata ya mallaki hankalin kan sa.

KALAMAN TOZARTA IYAYE DA SUNAN MURNA

A iyaka nazari na, wannan ya fi faruwa a jinsin mata – idan sun samu nasarar ribatar wani abu, ko lashe wata gasa, ko samun wani matsayi.

Sa’ilin da ‘wataƙila’ aka zo tattauna wa dasu akan yadda suka tsinci kansu a wannan muƙamin, ko nasarar; sai suce “ai lokacin dana fara wannan al’amarin, iyaye na ba sa so; kullum fada suke yi min…har baba na ma ya daina yi min magana…”

Wadansu kuma suce “wannan abu ina zaune nayi tunanin fara shi, amma gaskiya na samu ƙalubale sosai daga wurin iyaye na, domin har boye min ‘kaza-da-kaza’ dina suke yi – ni kuma na faki idanun su; na cigaba…”

Ko kuma suce “ai ita rayuwa duk abinda ka nufaci aikata wa, idan har zuciyar ka ta amince dashi, to kawai kayi. Lallai da na biye wa iyaye na da yan’uwa na; da ban kawo haka ba…” da sauran su dai.

Irin wadannan kalaman, duk lokacin da muka furta su a cikin jama’a fa, muna nuna wa Duniya ne cewa mun fi iyayen mu ‘Hangen Nesa’ ko ‘Sanin Makamar Rayuwa’ – wanda hakan zai iya janyo masu sauraro su zaci cewa maƙiyanmu na farko iyayen mu ne.

Har idan suna wurin taya mu murna ma, sai a riƙa cewa “da sun so su rusa masa rayuwa; ga shi yanzu sai wani murna suke…” wanda wannan a gani na ƙasƙanci ne; ba martabawa ba.

Wadansu ma, aure ne iyayen ta za su umurce ta dayi, sai ta ƙeƙasa ƙasa; ta nuna ba shine a gaban ta – maimakon haka sai ta fada wata harkar: ko sana’a, ko gwagwarmaya, ko wani abu. Yayin da aka zo jin yadda ta samu nasara; sai ta bayar da labarin yadda suka yi iyayen ta.

MENE NE ABIN YI?

Shi labari, kusan abu ne mai rai. Yana da kai; yana gangar jiki da hannuwa da kuma kafafu. Amma dai ya fi kama da bishiya mai rassa – wacce wani lokacin ko an sare wani reshen, bishiyar za ta rayu. Sabida haka, a lokacin bayar da labarin gumurzun rayuwa, ya kamata mu riƙa kiyaye bangaren da zai keta alfarmar iyayen mu.

Ya dace mu riƙa tsallake wa; ko barin wuraren – domin ba su da fa’ida sam. Mu sani cewa, yin hakan yana da tasiri sosai wajen ƙara bujire wa iyayen mu; da kuma koya wa ƙananan yara taurin kai, da hawa “kujerar na ƙi” idan an umurce su da suyi wani abinda suke ganin shine yafi dacewa dasu.

Iyaye fa suma mutane ne, amma daban suke. Domin ko kashe mu suka ce za suyi akan yi, ko barin wani abu (wanda basu fahimta ba), ba suna yi ne domin ba sa son nasarar mu a rayuwa bane. Abinda ake so kawai shine, mu samu lokacin yi masu bayani; su fahimta a hankali.

Duk abinda ba haka, a tunani na, nuna cewa ba ma mutunta ra’ayin su; ko dokar su ne…musamman idan ta kasance ma, tana da alaƙa da son dora mu akan hanyar gaskiya ne.

ABINDA YA KAMATA IYAYE SU RIƘA YI

Shi mutum, wani lokacin yakan samun dabara tayin wani abu, ba tare da ‘lallai’ wanin sa ya fada masa ba. Ubangiji Yana baiwa mutane wani hasken aikata, ko furta wani abu; wani lokacin. To idan iyaye sun fahimci yaron su yana da wata baiwa – wacce bata saba da ka’idar Addinin Musulunci ba, sai a ƙarfafa masa gwiwa. Haka ake yi.

Ba kasafai ake son komai iyaye su riƙa nuna isa da iko akan yara ba…musamman akan abinda suka fi nuna kwarewa; wanda zai taimaki rayuwar su – kuma bai ci karo da shari’a ba.