Muna nan a APC daram dam, karyan mahassada – Yari da Marafa

Tsohon gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari ya karyata raɗeraɗin da ake yaɗawa wai shi da Sanata Kabiru Marafa na shirin ficewa daga APC zuwa PDP.

Tsohon kwamishinan yaɗa labaran jihar kuma kakakin Yari ya shaida wa manema labarai a garin Gusau cewa ba gaskiya bane wannan labarai.

” Makiya da mahassada ne ke neman su sa Yari a gaba, amma karyan su, na gaba yayi gaba.

Haka shima sanata Kabiru Marafa, ya bayyana cewa bakin cikin har yanzu suna nan a APC daramdam ne yake kona wa wasu rai, ba su jin daɗi don ba haka suka so ba.

” Mu ɗinnan ne a kan gaba wajen kirkirowa da gina jam’iyyar APC tun daga bulo ɗaya har ya kai Shirgegen gida da kowa ke watayawa a ciki. Ba za mu bari wasu masu kwaɗayi da basu san hawa ba ballantana sauka su girbi abinda basu shuka ba.

” Muna da ƴancin mu halarci taro kowani iri ne tare da abokan mu daga kowanne bangare na siyasa. Eh, mun halarci taron bukin ɗaurin auren ɗiyar shugaban ƙungiyar Izala ta Kasa, Sheikh Bala Lau a masallacin Sultan Bello dake Kaduna.

Manyan malamai da ƴan siyasa siyasa da dama sun halarci taron ɗaurin auren ranar Juma’a a Kaduna.