IDAN AKA CI GABA DA BIYAN TALLAFIN FETUR: Najeriya za ta yi asarar naira tiriliyan 7 a 2023

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa idan aka ci gaba da biyan kuɗaɗen tallafin fetur, to a cikin 2023 Najeriya za ta yi asarar naira tiriliyan 6.72, wajen biyan kuɗaɗen tallafin man fetur.
Wannan bayani ya na cikin Daftarin Tsare-tsare Tasarifin Kuɗaɗe na Zangon 2023-2025 wanda Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ta gabatar a ranar Juma’a.
Tsawon shekaru kenan gwamnatin tarayya ta kasa samar da fetur a kan farashi mai sauki. Duk da Najeriya na cikin manyan ƙasashen da ke da ɗimbin arzikin fetur, shekaru da dama kenan ba a iya tace fetur a cikin ƙasar.
Najeriya ta dogara ne kacokan a kan shigo da fetur ɗin da ake amfani da shi a cikin ƙasar.
Hakan ya sa ana sayen litar mai da tsadar da tilas sai gwamnati ta riƙa biyan manyan dillalan fetur kuɗaɗen tallafin da idan ba don ana bada kuɗaɗen ba, to a yanzu haka lita ɗaya ta kai Naira kusan 400.
Daftarin da Minista Zainab ta gabatar na ƙunshe da bayar da shawarwari biyu: ko dai a ci gaba da biyan tallafin fetur har ƙarshen 2023, amma kuma a yi asarar Naira tiriliyan 6.72, ko kuma a ɗan rage asara, a raka har tsakiyar 2023.
Cikin 2022 dai Najeriya ta kashe Naira tiriliyan 4 wajen biyan tallafin fetur.
Cikin Janairu 2022 Najeriya ta yi sanarwar shirin cire tallafin fetur, amma ‘yan Najeriya su ka tayar da ƙayar-baya, aka janye cirewar.
Wannan labari ya zo daidai lokacin da gwamnatin tarayya ta ce bashin da ake biya duk wata ya fi kuɗin shigar da ake samu duk wata.
Hanyoyin samun kuɗaɗen shiga a Najeriya sun cukurkuɗe, ta yadda kuɗaɗen da ake ɗiba ana tsakura wa masu bin ƙasar bashi a duk wata, sun zarce kuɗaɗen shigar da ƙasar ke samu duk wata.
Wasu ƙididdigaggun bayanai na tasarifin kuɗaɗen Najeriya sun nuna cewa farkon 2022, wato daga Janairu har zuwa Afrilu, kuɗaɗen shigar da Najeriya ta samu, naira tiriliyan 1.63 ne kacal, yayin da bashin da ƙasar ta biya daga Janairu zuwa ƙarshen Afrilu ya kai naira tiriliyan 1.94. Hakan ya nuna an samu giɓi na naira biliyan 300 kenan.
Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Kasafi da Tsare-tsare Zainab Ahmed ce ta tabbatar da wannan labari a ranar Alhamis, tare da yin gargaɗin cewa akwai buƙatar gaggauta shawo kan matsalar samun kuɗaɗen shiga da kuma rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa a Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Ƙananan Hukumomi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ta yi kirdadon samun kuɗaɗen shiga har Naira tiriliyan 3.12 a cinikin ɗanyen mai da gas tsakanin 1 Ga Janairu zuwa 30 Ga Afrilu.
Sai dai kuma lamari ya lalace yayin da tara naira tiriliyan 3.12 ɗin bai yiwu ba, sai dai aka tara naira tiriliyan 1.23. Wato ko rabin kuɗaɗen da ake son tarawa ba a samu ba. Tunda kashi 39 bisa 100 kacal aka samu.
Duk fa da cewa farashin ɗanyen mai ya tashi a kasuwannin duniya, rahoton ya nuna tashin farashin bai tsinana wa Najeriya abin kirki ba, saboda an samu ragowar ɗanyen man da ake haƙowa, man kuma ya yi ƙaranci dalilin ɓarayin mai masu fasa bututu, masu satar ɗanyen mai su na tsallaka ruwa da shi da kuma kuɗaɗen tallafin fetur da Gwamnatin Tarayya ke biya saboda tsadar jigilar tataccen fetur daga Turai zuwa sauke shi a nan Najeriya.
Minista Zainab ta yi kiran a ruɓanya ƙoƙarin da ake yi wajen tara kuɗaɗen shiga na cikin gida.
Ƙididdiga ta nuna tsakanin Janairu zuwa ƙarshen Afrilu 2020, Najeriya ta bashin Naira biliyan 943.12. Amma kuma kuɗaɗen shiga Naira biliyan 950.56 ta samu. Kenan hakan na nufin kashi 99 na kuɗaɗen shigar waɗancan watanni huɗu, duk wajen biyan basussuka kuɗaɗen su ka tafi.
Sabuwar ƙididdiga ta ranar Alhamis ta nuna daga farkon Janairu zuwa ƙarshen Afrilu 2022 kuma, kuɗaɗen shiga daga fetur Naira biliyan 285.38 ne kacal. Kuɗaɗen da ba na fetur ba ne kuma sun kai Naira biliyan 634.56. An samu waɗannan kuɗaɗen daga harajin da ake danƙara wa kamfanoni, harajin kai-tsaye da harajin jiki magayi.
Najeriya ta shiga wani hali saboda ɓarkewar yaƙin Rasha da Ukraniya da kuma wasu dalilai na cikin gida.