ABIN DA KAMAR WUYA: Ace wai Peter Obi na jam’iyyar Labour ya yi nasara a zaben shugaban kasa – Atiku

Dan takarar shugaban ƙasa na jami’yyar PDP Atiku Abubakar ya ce zai zama abin mamaki da al’ajabi a ce wai yau Peter Obi na Jam’iyyar Labour yayi nasara a zaben shugaban kasa na 2023.
Atiku ya fadi haka ne da yake tattaunawa da talbijin din Arise TV.
Idan ba a manta ba da farko dai Peter Obi ya fito takarar shugaban ƙasa a jami’yyar PDP ne inda daga baya ya koma Jami’iyyar LP.
Obi ya koma Jami’iyyar LP ana kwanaki uku jami’yyar PDP ta yi zaben fidda gwani inda yake bayyana cewa ya fice ne saboda rudani da ya dabaibaye jam’iyyar a lokacin.
“Tsakani da Allah ban ganin jam’iyyar Labour za ta samu kuri’u fiye da PDP kamar yadda mutanen tiwita ke rurutawa saboda jam’iyyar LP Fanko ce bata watsu a kasar nan ba, bata gwamna ko daya ko yan majalisa wai har ace wai zata yi tasiri.
“ lallai zai zama abin mamaki da al’ajabi ace wai Peter Obi yayi nasara a zaben 2023.
“Sun ce suna da magoya baya sama da miliyan a shafukan sada zumunta amma kuma kuri’u naya suka samu a jiahr Osun, zaben gwamna da aka kammala kwanakwanan nan.
“A yankin arewa kusan kashi 90% na mutanen yankin basu shiga shafukan yanar gizo.
Atiku ya kuma ce Obi bai fada masa cewa zai bar jami’yyar PDP ba sai bayan kwanaki uku da komawar sa jami’yyar LP.
Atiku na daya daga cikin mutanen dake sukar kungiyar “OBIdient Movement” yana mai cewa kungiyar ta wuce gona da iri kuma ba ta da wani tsari tun daga farkon kafata ma.
Obi ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar, idan aka zabe shi shugaban kasa a 2023.