Cutar kwalera ta yi ajalin mutum biyar a jihar Kano

Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Kano ta bayyana cewa mutum 189 sun kamu da cutar kwalera sannan mutum biyar sun mutu a dalilin kamuwa da cutar a jihar.

Da yake ganawa da manema labarai ranar Talata a jihar kwamishinan lafiyar jihar Aminu Ibrahim ya ce wannan lissafi ne na tun daga watan Janairu zuwa Afrilu 2022.

” A ranar 16 ga Afrilu 2022 mun samu rahotan bullar cutar amai da gudawa a karamar hukumar Dambatta inda muka gudanar da bincike a kai.

” Dama kuma a baya akwai mutum 189 da suka kamu da cutar daga kananan hukumomi 20 a jihar. Daga ciki mutum 184 sun warke sannan cutar ta yi ajalin mutum biyar.

” Sanin kowa ne cewa cutar kwalera na yawan bulla a Najeriya musamman lokacin damina sannan, hakan na faruwa ne saboda rashin tsaftace muhalli, rashin amfani da ruwa mai tsafta, rashin tsaftace jiki da yin bahaya a waje.

Ya ce hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa an samu karin mutum 2,339 da suka kamu da cutar daga jihohi 30 daga watan Janairu zuwa Yuni 2022.

Ibrahim ya ce gaggwar daukan matakan dakile yaduwar cutar da gwamnati ta yi ya taimaka wajen hana yaduwar cutar a jihar.

” A bara mutum 12,116 ne suka kamu da cutar inda daga ciki mutum 329 suka mutu.

Ya ce gwamnatin Abdullahi Ganduje a shirye take ta tallafa wa mutane wajen dakile yaduwar cutar.

Ibrahim ya yi kira ga mutane da su kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin samar wa kansu kariya daga kamuwa da cutar.