Hukumar NDLEA ta kama haramtattun kwayoyi masu nauyin kilogiram 369.903kg da mutum 73 a Kaduna

Hukumar NDLEA ta kama haramtattun kwayoyi masu nauyin kilogiram 369.903kg da mutum 73 a jihar Kaduna.
Shugaban hukumar Ibrahim Barji ya sanar da haka ranar Alhamis yana mai cewa hukumar ta yi wadannan kamen ne a watan Yuni.
Barji ya ce a cikin wannan watan babban kotun tarayya dake Kaduna ta yanke wa mutum 7 masu safarar muggan kwayoyi hukunci.
Ya ce ganyen wiwi mai nauyin kilogiram 93.056, hodar ibilis, methamphetamine 0.030kg, tramadol 0.056kg na daga cikin muggan kwayoyi da hukumar ta kama.
Hukumar ta kuma kama bindiga kiran pistol mai lanba 7737 guda daya da karamar bindiga kira hannu guda daya.
“Hukumar ta rusa wuraren sha da safarar muggan kwayoyi a Kunku Rigasa, Rido, Mararaban Jos da Kasuwar Sati.
Barji ya ce hukumar za ta ci gaba da kai farmaki wajen hana sha da safarar muggan kwayoyi a jihar.