Hukumar NCC ta baiwa sansanin horas da daliban NYSC na Abuja gudunmawar katifu 100

A makon da ya gabata ne hukumar NCC ta baiwa sansanin horas da daliban NYSC k dake Kubwa Abuja.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Ikechukwu Adinde ya sanar da haka w
a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce hukumar ta baiwa sansanin gudunmawar katifu ne saboda kwashe su da matasa suka yi a lokacin Zanga-zangar EndSARS.

Adinde ya kuma ce a wannan ziyara da suka yi hukumar ta wayar da kan daliban NYSC kan su rungumi sana’o’in hannu.

Bayan haka hukumar ta kuma wayar da kan daliban NYSC kan aiyukkan sada zumunta da hukumar ke yi a kasar nan.

Adinde ya ce tun bayan bullowar cutar korona ƴan kasuwa sun koma amfani da kafafen sada zumunta a kasar nan.

Ya ce yin haka da ƴan kasuwan suka yi ya taimaka wajen bukasa kasuwanci sannan ya taimaka wajen kiyaye dokar gujewa kamuwa da cutar korona na bada tazara.

Sai dai kuma hakan ya haifar da barayi dake damfarar mutane ta yanar gizo.

A dalilin haka Adinde ya yi kira ga daliban da ma’aikatan hukumar NYSC da kada su bada bayanan asusun ajiyansu na banki ko kuma bayanai a kansu.