GARGADIN HUKUMAR LAFIYA TA DUNIYA: A yi hattara da darkakowar ‘korona mai harshen-damo’

Duk da cewa ana ci gaba da samun raguwar cutar korona tsawon makonni da dama a jere, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadin fuskantar wata sabuwar gagarimar matsalar korona da ka iya kunno kai a yanzu.

Darakta Janar na WHO, Tedro Ghebreyesus ne ya yi wannan gargadin a taron duk wata-wata da ya ke yi da manema labarai, a hedikwatar WHO da ke birnin Geneva.

Yayin da ya ke wannan gargadin, Tedro ya kuma yi rokon a kara bayan da tallafin gudummawar rigakafin korona ga kasashe masu tasowa.

Ya ci gaba da cewa rashin daidaito wajen raba rigakafin Korona zai iya haddasa ci gaba da yaduwar cutar a kasashen da ba su da galihun samun wadata rigakafin a kasashen da ba su da sukunin samun wadatacciyar allurar.

Ya ce hakan zai iya maida hannun agpgo baya, yadda rigakafin da aka yi wa kalilan daga cikin mutanen kasashen ba za ta yi wani tasiri ba.

“Rashin wadatar rigakafin korona a wasu kasashe, babbar barazana ce ga duniya ba karama ba.

“Ba kasashen da ba su yi rigakafin kadai matsalar za ta shafa ba. Har kasashe manya wadanda ke ganin kamar sun hau tudun-mun-tsira.”

Ya zuwa jiya Litinin dai korona ta kama mutum miliyan 173 a duniya, ta kashe mutum miliyan 3.7.

“Akwai damuwa a yanzu saboda korona da sake darkakar kasashen Afrika ta na yi masu duka da bulala mai harshen-damo. Haka ta sake dumfarar kasashen Amurka da na Ywmmacin Tekun Pacific.

“Yayin da kasashen da su ka ci gaba kuma su ka maida hankali wajen kawo karshen annobar a kasashen su, su kuma kasashen da ba su da galihun yin rigakafin na cikin barazanar da ka iya shafar wadanda ke bakin kokarin su.”

Yayin da WHO ta ce wadanda ba a yi wa rigakafin ba na cikin halin yiwuwar fuskantar matsaloli, manyan kasashe sun yi wa kashi 44% na mutanen rigakafi. Amma kasashe marasa galihu ko kashi 1% ba su yi wa rigakafi ba.