Hotuna: Buhari ya tafi wani muhimmin taro Amurka

Jirgin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya tashi zuwa birnin New York na ƙasar Amurka da safiyar yau Lahadi 19/9/2021 domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 76.

Bayan taron, shugaban ƙasa zai gana da wasu shuwagabbanin duniya da ƴan kasuwa da masu zuba jari.

Ana sa ran zai dawowar saa ranar Lahadin makon gobe.

An wallafa wannan Labari September 19, 2021 10:34 AM