Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN Mailafiya ya rasu

Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya Obadia Mailafiya ya mutu.

Rahotanni sun ce ya mutu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya duk da cewa har yanzu ba a gama tantancewa ba.

Daily Trust ta ruwaito An haife Obadia Mailaifiya a ƙauyen Randa dake ƙaramar hukumar Sanga na jihar Kaduna shekarar 1956.

Ya yi karatun Firamare zuwa Sakandare a ƙaramar hujumar Akwanga na jihar Nassarawa inda ya girma, kafin ya wuce zuwa Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Ya yi aiki da Bankin Cigaban Afirika kafin ya zama Mataimakin Babban Bankin Najeriya a shekarar 2005 zuwa 2007.

Shi ne wanda hukumar DSS ta gayyata a kwanakin baya bisa wani hiran da aka yi da shi a gidan Radion Wazobia a jihar Lagos in da ya ce akwai wani Gwamna dake ɗaukar nauyin Boko Haram.

An wallafa wannan Labari September 19, 2021 2:37 PM