HIMMA DAI MATA MANOMA: Yadda noman alayyahu da kiwon dabbobi ya su ka zama sanadin arzikin matar da ta yi aiki Amurka ta dawo

Nike Mbulu mace ce mai himmar noma. Har ma ta yi ƙarfin da yanzu haka ita ce Shugabar Accent Integrateg Farms a Lagos.

Mbulu ta mallaki filin da ta ke noma da kiwo har kamfaceciyar eka biyar inda ta ke noman alayyahu da kuma kiwon dabbobi.

Yanzu haka ta yi ƙarfin da har ma ta nada ma’aikatan dindindin mutum 11 da ke aiki a gonar ta.

Mbulu ba kifin-rijiya ba ce. Kafin ta kama noma haiƙan ta taɓa yin aiki a wani kamfanin hada-hadar kuɗaɗe a Amurka.

“Na fara noma bayan na yi aikin kamfani a nan Najeriya da kuma Amurka. Ma soma sha’awar noma ne bayan da gwamnatin Najeriya ta riƙa shiga harkar noma domin a faɗaɗa tattalin arziki da kuma karin samun kudaden shiga.

“To ni hankali na ya fi kwantawa ga noma saboda harka ce wadda ko da girma ya kama mutum ya na aiki ya yi ritaya, zai iya ci gaba da ita.

“A lokacin sai wani ya ce min ai Gwamnatin Jihar Lagos na bayar da filin noma. Na nema kuma na samu. Amma akwai sharaɗin cewa ga abin da za ka riƙa nomawa.”

Mbulu ta ci gaba da cewa, “na fara cikin 2015. Na fara da gina tafkuna guda 10.

“Na kusan shafe shekarar farko wajen shirye-shiryen gina tafkuna, kawo kayan aiki. Sai daga baya mu ka fara aniyar fara shuka da dashe cikin 2016.

“Ni na fi maida ƙarfi wajen noman alayyahu da sauran kayan miya na zamani.

Kuma ya kamata a sani cewa har kiwon kifi na ke yi fa.

Noman zamanin da na ke yi ba a gidan gilashi na yi wa allayahun shinge ba. Da raga na shincige alayyahun, domin rage masa hasken rana mai zafi.”

Ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa a yanzu haka ta na nan ta haƙilon ganin cewa ta samu kantamemiyar gona a Jihar Ogun daga hannun gwamnantin jihar.

“Ba mu fara fitar da kayan alayyahu da kayan miya a ƙasashen waje ba har yanzu tukuna. Saboda buƙatar sa a nan gida ta yi yawa sosai. Kuma na fi so mu riƙa fitar da abu gangariya. Na yanzu da mu ke nomawa ɗin ma gangariya ne, amma na fi so mu ƙara inganta shi kafin mu fara fitarwa zuwa ƙasashen ƙetare.

“Mu na fuskantar kalubale sosai. Domin a gaskiya mutum ya ce zai yi ko ma wane irin kasuwanci a Najeriya. Ba wai samun kuɗin aikin noman ne kaɗai ƙalubale ba. Samun ma’aikata da kayan aiki duk shi ma wani ƙalubale ne.

Ta ƙara da cewa ba ta da matsala wajen samun takin zamani da iri da kuma sinadarin ‘chemicals’.

Inda mu ka samu matsala kuma shine hana shigo da sinadaran kemicals da a baya aka yi zargin Boko Haram na samun sinadaran su na haɗa bama-bamai da su.”

Ta ƙara da cewa ba ta taɓa amfana da tsare-tsaren gwamnati ba, saboda akasari ana yin tsare-tsare da tallafi ga matasan da ba su wuce shekara 18 zuwa 35 ba.