Masu neman su ɓalle daga Najeriya na da damar yin haka – Kakakin majalisar Legas

Kakakin majalisar Dokokin jihar Legas Mudassir Obasa, ya bayyana cewa babu laifin wasu da ke ganin zaman su a kasa tare da wasu ya ishe su su nemi ware wa.
Obasa ya ce dole jami’an tsaro su rika daga wa masu zanga-zanga kafa domin doka ce ta basu damar yin haka.
” Ba kawai a zaɓe mu bane shikenan an gama, suma waɗanda suka zaɓe mu na da daman yin zanga-zangar neman a biya musu wata buƙata ta su ba tare da an muzguna musu ba.
” Haka nan kuma suma gwamnatocin yankin kudu da suka ayyana bukatunsu ga sauran ƴan kasa, su tabbata ba su koma gida sun kwanta bacci ba, su bi bukatunnan sauda kafa domin ganin ya tabbata.
Mambobin majalisar jihar da suka yi jawabi a zauren Majalisar sun bayyan cewa lallai akwai gyara a kundin tsarin mulkin Najeriya wacce ake amfani da ita a kasa yanzu.
Sun bayyana cewa muddun ba kundin tsarin mulkin ƙasar ba ce aka yi mata garambawul ba za a samu cigaba mai amfani a kasarnan ba.
A karshe Obasa, ya ce dole a yi murnar shekaru 22 da dawowar dimokraɗiyya a kasar nan ya na fatan za a ci gababda samun ci gaba mai daurewa.