HIMMA DAI MANOMA: Yadda manoman Najeriya ke rungumar dabarun noman kauce wa ƙalubalen canjin yanayi

Orija Oladimeji hamshaƙin manomi ne a Jihar Kwara, wanda ya shafe shekaru ya na idan ya yi noma sai ya girbi asara.

Babban dalilin da ke sa Oladimeji ke ɗibga asara, shi ne riƙo da ya yi da tsoron tsarin noman da ya gada daga iyaye da kakanni, wanda ake amfani da fartanya, garma, kalme da adda.

Amma labari ya sha bamban ga Akanbi, inda ya riƙa samun nasibin noma ya yin da ya rungumi sabon tsarin noman zamani na ‘greenhouse’. Kuma shi ne mutumin farko da ya fara yin sabon salon noman a ƙauyen su, wato Akanbi Ade a Jihar Kwara.

“Na rungumi wannan sabon tsarin noma ne saboda ƙalubalen canjin yanayin da manoma kan fuskanta a yankin mu.” Haka ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Ya ce ya rungumi noman ‘greenhouse’ ne saboda asarar da ya ke cin karo da ita a noma na gargajiya, sakamakon canjin yanayi da kan shafi kayan abincin da ake nomawa.

Ya ce a Cibiyar Koyar Da Dabarun Noma (IITA) ya koyi wannan dabara ta noman zamani.

“Saboda yanayi a wannan yankin duniya ta mu, akwai zafi sosai. Idan yanayi ya sauya kuma shi ke haifar wa manoma babbar matsala. Wani lokaci tsananin zafi ya yi wa shuka illa. Idan sanyi ya zo kuma, shi ma idan ya yi yawa ya na illata shuka a gona.

“To dalili kenan mu ka rungumi tsarin noma na ‘greenhouse’.”

‘Greenhouse’: Tsarin noma ne da ake wa canjin yanayi dabarar yadda ba zai shafi shuke-shuke ba. Sanyi ko zafi ba za su yi wata illa ga tsarin ‘greenhouse’ ba.

Wato ana yin amfani ne da irin shuka na zamani, sai a shuka shi a keɓantaccen wurin da aka yi wa rumfa ko aka kewaye da shinge ko waya ko katanga, inda rana ko sanyi ko wani canjin yanayi ba zai yi masa wata illa ba.

Wannan tsari kuma ya na kawar da matsalar barazanar fari ko ƙwari ko wasu cututtuka masu lalata shuka da kayan noma.

Oladimeji wanda shi ya kafa Ibujeran Farms, ya ce a yanzu kam ya na samun riba sosai mai tarin yawa a sabon tsari noman da ya runguma na ‘greenhouse’.

Ya ce a wannan shekara ya samu tumatir zai kai yawan cikin ƙaramin kwandon tumatir 300.

Kuma ya ce a yanzu haka ya na ta shirin faɗaɗa wannan tsarin noman a cikin makekiyar gonar sa.

Ya ce amfanin gonar da aka noma ta hanyar ‘greenhouse’, ya fi ɗaukar tsawon lokaci bai lalace ba, fiye da wanda aka noma a gona.

“Za ka iya ajiye tumatir ɗin gonar ‘greenhouse’ a kan tebur tsawon kwana 21 bai lalace ko ya ruɓe ba. Ba kamar wanda aka noma a gona ba, wanda idan ba ka saka shi a firji ba, kwana biyu ko uku ruɓewa zai yi.”

Ya ƙara da cewa muhimmancin noman ‘greenhouse’ shi ne manomi ya san yawan ribar da zai iya samu tun ma kafin ya yi girbi, idan dai ya bi matakan da aka gindiya sosai.

Sai dai kuma ya ce a wanann tsari akwai matsalar tsadar irin shuka. Kuma sai ka biya kuɗi an horas da waɗanda za su riƙa yi maka aikin kula da shukar ka.

Manoma da dama da wannan jarida ta yi hira da su, sun shaida mata ce sun yanke shawarar su rungumi tsarin noman zamani na ‘greenhouse’ ne domin kauce wa barazanar da canjin yanayi ke yi wa amfanin gona a gonakin su.

Binciken SBM Intel ys nuna cewa kashi 79 na manoman Najeriya waɗanda su ka noma kayan marmari, kayan miya, rogo da masara kusan duk matsalar canjin yanayi ya janyo masu yin asara sosai. Musamman ƙarancin ruwan sama da kuma ambaliya a cikin 2020.

An gudanar da wannan bincike ne a cikin jihohi bakwai ciki har da Benuwai, Nassarawa, Osun, Katsina.