AREWA A HANNUN ‘YAN BINDIGA: Yadda mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara ya mutu a hannun ƴan bindiga, bayan ya shafe watanni biyu a tsare

Mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara, Mu’azu Magarya ya mutu a hannun ‘yan bindiga, bayan ya shafe sama da watanni biyu a tsare.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda aka sace shi tare da kawun kakakin da kishiyar mahaifiyar kakakin da kuma wasu ‘yan uwan sa huɗu a ƙauyen Magarya, lokacin da aka kai wani hari a gidan mahaifin kakakin.

Gogarman ‘yan bindiga Turji ne ya tura yaran sa su ka kamo su.

Bayan kama su, an yi ƙoƙarin karɓo su ta hannun wani ɗan bindiga Halilu Kachalla, amma ba a samu nasara ba.

Daga baya kuma an kai kuɗin fansa a daji a sansanin Turji, amma yaron sa mai suna Ɗanbokkolo ya ce Turji ya ce a koma da kuɗin, ya fasa sakin mahaifin kakakin.

Da ya ke wa manema labarai bayani a Hedikwatar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara bayan da sojoji su ka ceto su, kawun Kakakin Majalisar Zamfara mai suna Ɗahiru Sarki, ya ce bayan an ceto su, Kachalla ya sanar da shi cewa ɗan’uwan sa, wato mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara, ya mutu sanadiyyar bugun zuciya a hannun su Turji.

An kama Ɗahiru da mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara a gidan sa da ke ƙauyen Magarya. Amma bayan wata biyu sojoji sun ceto mutum huɗu.

Ɗahiru ya sanar da manema labarai cewa ba a sansani ɗaya aka tsare shi da mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara ba.

Wani hadimin Kakakin Majalisar Zamfara da ba ya so a ambaci sunan sa, ya shaida wa wakilin mu cewa shi kan sa Kakakin Majalisar ya shiga damuwa bayan da su Turji su ka ƙi karɓar kuɗin fansa. Ya yi tunanin ko mahaifin sa ya mutu kafin a kai kuɗin fansar.

Yadda Gogarman ‘Yan Bindiga Turji Ya Ƙi Karɓar Kuɗin Fansar Sakin Mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara:

‘Yan bindigar da su ka sace mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara sun raina kuɗin fansar da aka ba su, saboda haka sun ƙi sakin sa.

An dai kama mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara Honorabul Nasiru Magarya tun a farkon watan Agusta, a wani farmaki da ‘yan bindiga su ka kai a Magarya.

An kama shi tare da wasu mutum biyar da su ka haɗa har da matar mahaifin na sa, a Magarya da ke cikin Ƙaramar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.

Wasu jami’an gwamnati sun nemi gogarman ‘yan bindiga Halilu Kachalla domin ya shiga tsakani, ya taimaka waɗanda su ka kama mahaifin kakakin su sake shi.

Wani hadimin Kakakin Majalisar Zamfara ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an gayyaci Kachalla ya ne ta hannun wani jami’in Ƙaramar Hukumar Shinkafi.

‘Yan Bindiga Sun Raina Kuɗin Fansa

Wani hadimin Kakakin Majalisar Zamfara ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa makusancin kakakin ya samo kuɗi kamar yadda ‘yan bindiga su ka nema.

“Tsohon Kwamishina wanda ɗan Zurmi ne ya na a sahun gaba wajen sasantawar. Shi ma Halilu Kachalla ya yi bakin ƙoƙarin sa, amma ka san ya na da matsala da sauran ‘yan bindiga, saboda a yanzu ya fi kusa da gwamnatin Zamfara.

“Sai shi tsohon kwamishina ya shaida wa Kakakin Majalisa cewa za su biya kuɗin kawai, tunda Kachalla ya kasa taimakawa a sako mahaifin kakakin.”

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa bai san ki nawa maƙudan kuɗaɗen da aka haɗa wa ‘yan bindigar ba.

“Abinda kawai na sani, wasu mutane daga Zurmi da Shinkafi sun ɗauki kuɗi sun kai a sansanin gogarma Turji, amma ba ma ko samu ganin sa ba. Sun dai gana da wani kwamandan sa mai suna Ɗan Bukkolo, wanda shi kuma ya shaida masu cewa umarnin da Turji ya ba shi kawai idan sun zo su koma da kuɗin.”

Lamarin ya faru kwana kaɗan bayan ‘yan bindiga sun sake yin tattaki har Magarya, su ka ƙone gidaje da dama, ciki har da gidan mahaifin Kakakin Majalisa wanda ke a hannun su da kuma wani gidan kawun kakakin.

Wakilin mu ya kasa samun Kakakin Yaɗa Labarai na Kakakin Majalisar Zamfara, mai suna Mustafa Ƙaura, domin jin halin da ake ciki, saboda matsalar kulle lambobin wayoyi da aka yi a Zamfara.