HATTARA JAMA’A: Ana yaɗa labarun Ƙarya akan Tinubu

Kwamitin Kamfen din ɗan takarar shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya bankaɗo wasu rahotanni da labaran karya da ake yaɗawa a musamman shafukan sada zumunta na Facebook na karya akan Bola Tinubu waɗanda da ba gaskiya bane.
A martani da kwamitin ya fitar wanda Mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga Bola Tinubu, AbdulAziz AbdulAziz ya saka wa hannu, an yi kira ga mutane su yi watsi da irin waɗannan labarai cewa ba gaskiya bane.
” Mun lura da wasu shafukan labarai na bogi musamman a Facebook suna yaɗa wani labarin ƙarya da yarfe irin na siyasa wanda suke rawaito cewa wai an kama wasu motoci da kuɗaɗe mallaki ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC.”
Karanta nan
ANA YAƊA LABARUN ƘARYA AKAN ASIWAJU AHMED BOLA TINUBU
Mun lura da wasu shafukan labarai na bogi musamman a Facebook suna yaɗa wani labarin ƙarya da yarfe irin na siyasa wanda suke rawaito cewa wai an kama wasu motoci da kuɗaɗe mallaki ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC.
Wannan magana ƙarya ce tsagwaronta wanda maƙiya suka shirya domin fata sunan Alhaji Ahmed Bola Tinubu.
Abin lura a nan shi ne babu wata madogara da su waɗannan masu yaɗa labaran ƙarya suka dogara da ita wajen rawaito wannan magana ta bogi.
Muna Jan hankali mutane da su lura da cewa a kwanakin da suka rage mana kafin shiga zaɓe ƴan siyasa marasa tsoron Allah da dama za su yi ta Ƙoƙarin yaɗa labaran ƙarya da sharri domin ɓata sunan abokan hamayyar su da suke ganin cewa ba za su iya kayarda da su a akwatin zaɓe ba sai sun haɗa da ƙarya da sharri domin ɓata musu suna.
Ɗan takarar jam’iyyar APC, Jabagan Borgu ya sha faɗar cewa shi bai yarda da yin sharri ko yarfen siyasa ba domin ba sahihiyar hanya ce ta cin zaɓe ba. Abinda muka dogara da shi shi ne a bar mutane su yi zaɓin ɗan takarar da suka ga ya dace kuma yana da ƙwarewar aiki da zai iya kawowa ƙasa cigaba, ba tare da an bi haramtaciyyar hanya ba wajen ru&ar da tunanin masu zaɓe.
Muna kira ga jama’a da su yi watsi da wannan labarin bogi marar hujja wanda wasu maƙiya kuma marasa son zaman lafiya suka ƙirƙira.
Sa HannuAbdulaziz AbdulazizMataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu29/1/2023