GARGADI: NAFDAC ta gargadi mutane kan shan kwayoyin rage kiba

Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kasa NAFDAC ta gargadi mutane kan shan kwayoyin maganin dake rage kiba.

Shugaban hukumar Mojisola Adeyeye ta yi wannan gargadi ne a wata wasika dake dauke da lamba 049/2022 da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta buga a shafinta.

Mojisola ta ce ta yi wannan gargadi saboda kwayoyin dake rage kiba na kawo cutar Sankara a jiki.

Ta ce sakamakon binciken da hukumar ta gudanar game da wani maganin rage kiba da Kamfanin sarrafa magunguna na ‘Ingi Oman’ ya ke yi ya nuna cewa maganin na dauke da sinadarin ‘phenolphthalein’ wanda hukumar kula da ingancin magunguna da abinci na kasar Amurka ta hana amfani da shi.

Mojisola ta ce zuwa yanzu wannan magani ta basu a kasuwani da kafafen sada zumunta dake yanar gizo.

Ta ce baya ga kawo cutar Sankara da phenolphthalein ke yi sinadarin na cutar da kwayoyin halitan mutum.

Mojisola ta yi kira ga mutane musamman wadanda suke siyar da maganin ko suke amfani da shi da su yi gaggawan Kai maganin ofishin NAFDAC mafi kusa da su.

Ta kuma ce za a iya tuntubar hukumar ta yanar gizo ko ta wayar salula idan har an samu matsaloli a dalilin amfani da maganin.