Gwamnatin Nasarawa za ta yi wa ƴan mata masu shekaru 9-14 rigakafin cutar daji

Gwamnatin Nasarawa ta bayyana cewa za ta yi wa ƴan mata masu shekara 9-14 allurar rigakafin cutar daji don kare su daga kamuwa da cutar dajin dake kama mahaifa da nono.

Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na jihar Mohammed Addis ya sanar da haka ranar Alhamis bayan an tashi zaman da ya yi da masu ruwa da tsaki a jihar.

Addis ya ce jihar Nasarawa na daga cikin jihohi 16 da aka zaba domin yi wa mata allurar rigakafin cutar daji a kasar nan.

Ya jinjina namijin kokarin da Shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnan jihar Abdullahi Sule da Shugaban hukumar NPHCDA Fa’Isal Shua’Ib suka yi wajen ganin sun samar da maganin rigakafin domin inganta lafiyar mata a jihar.

Addis ya ce cutar dajin dake kama nono da mahaifa na daga cikin cututtukan dake kisan kashi 50% na mata a Najeriya.

Sakamakon binciken da NDHS ta gudanar a shekarar 2018 ya nuna cewa daga cikin mata 10 dake kamuwa da wadannan cututtuka mutum biyu ne kadai ke warkewa.

“Domin samar wa mata kariya daga kamuwa da cututtukan ne ya sa aka hada maganin rigakafin.

“Za a dauki kwanaki 7 domin yi wa ’yan mata allurar rigakafin a kananan hukumomi 13 dake jihar.

“Jami’an lafiya za su bi gida-gida, makarantu da coci da masallaci domin yi wa mata allurar rigakafin cutar.