Ƴan sanda sun kama dattijo mai shekaru 84 da ya kashe matarsa saboda ta hana shi saduwa da ita

Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta kama Gabriel Ahuwa mai shekara 84 bayan ya kashe matarsa mai shekara 75 saboda ta kaurace masa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Chidi Nwabuzor ya sanar da haka a garin Benin ranar Alhamis.
Nwabuzor ya ce Ahuwa na daga cikin batagari 198 din da rundunar ta kama masu aikata laifuka da suka hada da fashi da makami, kisa da garkuwa da mutane a jihar.
Ya ce ko da Ahuwa ya shiga hannun jami’an tsaro bai nuna ya yi nadamar kashe matarsa da ya yi ba domin a ganin sa abinda ya kamata ya yi kenan.
“Mata ta ba ta jin magana na na da ƴaƴa 7 amma duk lokacin da na nemi mu sadu sai ta ki ba ni hadin kai.
“Na kai karanta wajen iyayen ta da ‘yan uwa na amma duk ta ki bani hadin kai sannan na ji labarin cewa tana kwana da wasu fastoci a coci ne ya sa taki kin bani haɗin kai.
Nwabuzor ya ce Ahuwa na tsare a ofishinsu sannan idan a ka kammala bincike za su maka shi kotu domin yanke masa hukunci.