Dalilan rashin raba tallafi ga jihohi 31, waɗanda ambaliyar 2022 ta shafa – Majalisar Tattalin Arziki

An bayyana dalilin da ya sa har yau Gwamnatin Tarayya ba ta raba wa waɗanda ambaliyar ruwa ta yi wa ta’adi ba, tun a cikin 2022, duk kuwa da alƙawarin da gwamnatin ya yi a wancan lokacin.
Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ne ya bayyana dalilan a cikin rahoton da ya karanta a zauren taron Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa, a ranar Laraba, a Fadar Shugaban Ƙasa.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ne shugabanci taron, indaa wurin har aka bayyana cewa an bai wa kowace jiha Naira biliyan 3 domin ta raba wa marasa galihu, ta yadda za a rage masu raɗaɗin tsadar rayuwar da suka shiga, tun bayan cire tallafin fetur.
Da ya ke jawabi, a cikin rahoton sa, Yahaya Bello ya ce ambaliyar 2020 ta ci rayuka sama da 600 a faɗin ƙasar nan.
Ya ce ambaliyar ta faru a jihohi 31, tare da lalata gidaje, gonaki da kayan abinci.
“Bayan Majalisar Tattalin Arziki ta kafa kwamitin mutum biyar da ya ƙunshi Gwamnonin Kogi, Jigawa, Anambra, Bayelsa, Legas da Yobe, an ƙara wa kwamitin mambobi da suka haɗa da: Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Ministan Gona, Ministan Ruwa, Minsitar Agaji da Jinƙai, Gwamnan Babban Bankin Najeriya da Daraktan NEMA”
Yahaya Bello a matsayin sa na shugaban kwamiti, ya yi ƙorafin cewa “daga cikin jihohi 31 da ambaliyar ta shafa, har yau 16 kaɗai suka gabatar da rahoton takamaiman yadda ambaliyar ta shafe su, ballantana a san irin yadda za a ware tallafin da ya dace da su.
“Har yau jihohi 15 ba su ba su bayar da rahoton da kwamitin mu ya ce su bayar ba, ballantana a san irin ɓarna ko asarar da aka yi a jihohin.
“Sannan kuma bayanan da wasu jihohin suka bayar bai yi daidai da abin da irin bayanan da kwamitin ke so su bayar ba.
“Wasu jihohin waɗanda su ka bayar da na su rahoton, su kan su ba su fayyace buƙatun kuɗaɗen da za ba su na tallafi ba, kuma ba su tantance waɗanda ya kamata a bai wa kuɗaɗen tallafin ba.” Inji Yahaya Bello.