Gwamnati ta kirkiro wani shiri don dakile yaduwar Kanjamau a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta kadamar da shirin dakile yaduwar cutar kanjamau a kasar nan mai taken ‘Youthful Alive and Healthy (YAaH Naija)’

Shugaban hukumar dake Yaduwar cutar kanjamau na kasa NACA Gambo Aliyu ya bayyana cewa shirin wanda zai a yi amfani da yanar gizo zai mai da hankali ne wajen wayar da mutanen da suka fi kamuwa da cutar hanyoyin da za su kiyaye domin samun kariya.

Aliyu ya ce shirin ya haɗa da wayar da kan mutane musamman matasa yin gwajin cutar ta hanyar bada kayan yin gwajin cutar domin mutane su rika yi wa kansu gwajin cutar sannan da karfafa gwiwowin mutane wajen yin amfani da maganin kare mutum daga kamuwa da cutar wato ‘PrEP’.

Ya ce maida hankali wajen dakile Yaduwar cutar a tsakanin matasa na daga cikin hanyoyin da zai taimaka wa kasan wajen rage yaduwar cutar a Najeriya.

Sakamakon binciken da Mode Of Transmission MOT ta gudanar ya nuna cewa matasa marasa aure sun fi kamuwa da cutar.

Sannan bada kayan yin gwajin cutar da karfafa gwiwowin su wajen yin amfani da maganin PrEP na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen kare matasa daga kamuwa da cutar.

Bayan haka a taron shugaban UNAIDS a Najeriya Leo Zekeng ya ce wannan shiri da gwamnati ta kirkiro shiri ne da zai taimaka wajen karkato da hankalin matasa din kare kansu daga kamuwa da kanjamau.

Zekeng ya ce ko da yake an samu ci gaba a dakile yaduwar cutar amma har yanzu akwai sauran aiki saboda rashin jawo hankalin matasa.

A shekaran 2021 yara da manya sama da miliyan 38 sun kamu da kanjamau a duniya. Hakan ya nuna cewa a shekaran 2021 mutum miliyan 1.5 ne suka kara kamuwa da cutar a duniya.

Sannan a shekaran 2022 kanjamau ta yi ajalin mutum 659,000 a duniya.

Ya ce rashin karkato da hankalin matasa kan hanyoyin guje wa kamuwa da cutar na daga cikin matsalolin dakile yaduwar cutar da Najeriya ke fama da shi.

Ya ce matasa masu shekara 15 zuwa 24 na da kason kashi 15% a adadin yawan mutane a duniya sannan suna da kason kashi uku a cikin yawan mutanen da suka kamu da kanjamau a duniya.

Matasa musamman mata sun fi kamuwa da cutar sannan wayar da kan matasa kan kanjamau yana nan a kashi 29%.

Zekeng ya ce kamata ya yi a wayar da kan matasa kan hanyoyin samun kariya daga kamuwa da kanjamau domin samun matasa da suke da koshin lafiya hanyar ce samar da zuri’a masu lafiya nan gaba.