KWAMACALA A APC: Shugaban jam’iyya Adamu ya zargi Tinubu da karya alƙawari, ya ce bai yi hakan ba

Sati ɗaya bayan Gwamnonin APC sun yi fatali da jerin sunayen Rundunar Kamfen ɗin Bola Tinubu ta APC 2023, shi ma Shugaban Jam’iyyar APC Abdulalhi Adamu ya zargi Tinubu da karya alƙawarin da ya yi bisa yarjejeniya kan batun sunayen dakarun kamfen ɗin na shugaban ƙasa.
Cikin wasiƙar da Adamu ya rubuta, ya ce Tinubu ya karya yarjejeniya ta hanyar ƙin saka sunayen Shugabannin Kwamitin Zartaswar APC (NWC) a cikin rundunar kamfen.
Irin haka ɗin ne ya harzuƙa wasu gwamnonin APC har su ka yi barazanar yi wa kamfen ɗin Tinubu ƙafar-ungulu.
Wannan matsaya da gwamnonin APC su ka cimma ce ta haifar da dakatar da fara kamfen ɗin APC har sai yadda hali ya yi, domin a shawo kan matsalar.
Yanzu haka ma duk da an fara kamfen tun daga ranar Laraba kamar yadda INEC ta bayar da izni, APC ta ɗage ranar fara kamfen a Jihar Kwara. Sannan kuma shi kan sa Tinubu ba ya ƙasar, ya garzaya Landan.
Cikin wasiƙar da Adamu ya rubuta da kakkausan harshe, ya ce ya yi da-na-sanin jin labarin yadda Tinubu ya watsar da sunayen NWC na APC, aka ware su daga cikin tawagar kamfen.
Adamu ya ce sai da dama ba sau ɗaya ko sau biyu ba, Tinubu ya sha yi masu alƙawarin yin aikin kamfen tare da Kwamitin Zartaswa na APC.
A can baya dai Abdulalhi da Tinubu sun ƙaryata masu cewa akwai saɓani a tsakanin su.
To amma kuma abin da ya faru biyo bayan fitar da sunayen rundunar kamfen ya nuna akwai wata-a-ƙasa a tsakanin su.
Tun da farko dai shi Adamu ya so Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ne aka tsayar takara ba Tinubu ba.
Adamu dai ya rubuta wa Tinubu wasiƙa ce a madadin ɗaukacin Kwamitin Zartaswa na APC, wadda ya bayyana cewa ba za su iya yin shiru ba, tilas ce ta sa su rubuta masa wasiƙar.
Ya ce “sunayen ‘yan kamfen ɗin abin mamaki ne, abin takaici kuma cike ya ke da karya alƙawari da saɓa yarjejeniya da aka yi da Tinubu.”
A Adamu ya fito ɓaro-ɓaro ya tunatar da Tinubu wuraren da su ka zauna ya yi masu alƙawarin a ofishin Adamu da kuma zaman su a Ɗakin Taro na NWC a Babbar Sakatariyar APC ta Ƙasa, a ranar 7 Ga Satumba, 2022.
“Ita fa nasarar zaɓe tilas sai da sa hannun kowa da gudummawar sa ta ke tabbata. Saboda haka kaucewa ko saɓa alƙawari na iya haifar da shakku ga ‘yan jam’iyya a faɗin ƙasar nan, tun ma tafiya ba ta yi nisa ba.”
Adamu ya musanta haka
Sai dai kuma shugaban jam’iyyar, Adamu ya karyata wannan wasiƙa, ya ce ba daga ofishin sa bane ta fito.
” Ban san da wannan wasiƙa ba sannan ba san daga inda ta fito ba. Saboda haka ina kira ga ƴan Najeriya su yi watsi da haka.
P