Gwamnan Zamfara ya sallami dukkan masu bashi shawara

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya sanar da sallamar dukkan masu bashi shawara na musamman.

Sanarwar hakan na ƙunshe cikin wata takarda da ta fito daga ofishin muƙaddashin sakataren gwamnatin jihar Alhaji Kabiru Balarabe a daren jiya Asabar.

A cewar sanarwar, wannan matakin ya biyo bayan sauya sheƙar gwamnan zuwa APC tare da ƙoƙarin kawo sauye ganin cewa gwamnatin sa ta ƙara jawo waɗanda suka cancanta domin bada gudumawarsu a tafiyar da gwamnatinsa ba tare da la’akari da jam’iyar da za su fito ba.

A cewar skataren gwamnatin jihar, mai baiwa gwamnan shawara kan harkokin tsaro baya daga cikin waɗanda sallamar ta shafa. Sannan gwamnan ya umarci waɗanda aka sallama da su miƙa ragamar gudanar da ofisoshin su da kayakin gwamnati dake hannayen su ga darakta janar na ofisoahin su ko kuma babban jami’in gwamnati dake nan.

Daga ƙarahe ya miƙa godiya garesu bisa gudumawar da suka baiwa gwambatin sa a iya lokacin da suka ɗauka suna gudanar da ofisoshin su.