KISAN KAI: Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa a Kano

Kotu a jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Salisu Muhammad-Yakasai hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Salisu na da shekaru 20 ne a duniya.

Kotu ta kama Salisu da laifin aikata kisan kai, bayan gamusuwa da hujojin da aka gabatar a gabanta kuma suka tabbatar Muhammad-Yakasai ya kashe Kociyan sa na kwallon kafa.

Lauyan da ya shigar da karar, Lamido Soron Dinki ya bayyana cewa Muhammad -Yakasai ya kashe kochiyan da ke horas da su wasan kwallon kafa mai da shekaru 32 ranar 2 ga Maris din 2019 a Gangare dake kwatas din Yakasai.

Ya abin ya faru ne da wajen karfe 11:20 na dare.

Shi kociyan da Muhammad-Yakasai suna hira sai sabani ya shiga tsakani suka barke da musu, cikin fushi Muhammad-Yakasai ya zaro wuka ya luma wa Kochiyan na sa a kirjin sa har sau biyu.

“An gaggauta kai Koch din asibitin Murtala Muhammad sai dai kash, likita ya tabbatar musu cewa Salisu ya rasu.

A kotun Soron Dinki ya gabatar da shaidu hudu amma kuma lauyan dake kare Muhammad-Yakasai, Sani Ibrahim-Salisu, ya gabatar da shaidu guda uku kadai.

Laifin da Muhammad -Yakasai ya aikata ya karya dokar ‘Penal Code’ na 221.