Gudun za a yi min auren-wuri ya sa na shiga aikin soja – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya shiga aikin soja ne domin kauce wa matsin-lamba da takurawar da iyayen sa su ka riƙa yi masa na ya yi aure.
Da ya ke jawabi a Fadar Sarkin Daura bayan ya ƙaddamar da titina biyu, Buhari ya ce duk wata ƙaddarar da ta samu mutum, ƙasa ko duniya baki ɗaya, to daga Allah Ta’ala ta ke.
A ranar Juma’a ce Buhari ya yi wanann jawabi, ya na mai yin godiyar musamman ga Allah Ta’ala, saboda tsawoncin ran da ya yi masa, har ya tsallake ibtila’o’in gaganiyar rayuwa daban-daban, daga lokacin da ya shiga aikin soja zuwa yanzu.
Musamman Buhari ya riƙa bayar da labarin irin yadda Allah ya riƙa tsarar da shi a lokacin Yaƙin Basasa, wato Yaƙin Biafra, ko kuma yaƙin Ojukwu.
Buhari ya buɗe ayyuka a Babban Asibitin Musawa, Sakandaren Gwamnati ta Musawa, Titin Gora-Maƙauraci-Malamawa da kuma Titin Sandamu-Ɓaure-Babban Mutum, sai kuma Titin Gurjiya-Ƙarƙarku-Sandamu a yankin Daura.
“Wannan dama da na samu har na shugabanci ƙasar nan, ta zo ne daga Allah Ta’ala.
“A duk duniya an san Najeriya a matsayin ƙasa mai yawan al’umma daban-daban mabambanta, masu bin addinai da al’adu daban-daban.
“An kuma san mu saboda mu na da ɗimbin yawan al’umma a ƙasar nan.
“Al’amarin Allah ne da rahamar sa har ya ƙaddara aka samu Shugaban Najeriya ya fito daga Daura,” inji Buhari.
Buhari ya ce ya bar aikin farko da ya fara samu a Daura, ya gudu ya shiga aikin soja, saboda kara a yi masa auren-wuri.
“Na shaida wa Gwamna Masari cewa na bar Daura na shiga aikin soja. Kuma daga nan Allah ya ci gaba da tsara min rayuwa ta a kan layin da ya kawo ni har matsayin da na ke a yanzu.
“Mu na tsara wa kan mu wani abu da mu ke so, Allah kuma ya na tsara mana mafificin abin da ya fi dacewa da mu. Haka ƙaddara ke kasancewa kan bawa daga Allah Ta’ala.
“Na kasance ina sahun gaba a filin yaƙin Basasa, na ga yadda dakaru da dama su ka kwanta dama. Wasu ma a gaba na su ka riƙa faɗuwa a lokacin da aka bindige su. Wasu kuma a gefe na. Amma Allah ya kuɓutar da ni, sannan kuma ya yi min tsawon rai.
“A wasu wuraren mun isa mun samu ba a daɗe da tarwatsa gadoji da bam ba. Wasu gadojin kuma an tarwatsa su da bam bayan mu tsallaka. Mun isa wasu wurare na ga gawarwakin sojoji abokan aikin mu birjik.
“Amma ni ga ni har yau da rai na. Wannan kuma wata ƙaddara ce ta Allah Ta’ala.”
Ya ce Masarautar Daura ta samu shahara daga ƙudirar Allah Ta’ala, ba daga wani ƙoƙari ko hoɓɓasan wani mutum ba.
Buhari ya yi alƙawarin cewa idan ya kammala mulkin sa, zai koma Daura ya yi zaman sa, bayan 29 Ga Mayu, 2023.