GUDUN TSIRA: Yadda aka tattake yara kanana yayin gudun tsere wa ‘ƴan bindiga a Katsina

A ranar Alhamis ne wasu yara 7 suka rasa rayukansu a kauyen Shimfida dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina yayin gudun tsere wa harin ƴan bindiga.

Mazauna kauyen Shimfida sun bayyana cewa wannan hari ya biyo bayan cire sojoji da aka yi ne a ƙauyen.

Wani shugaban kungiya Adam Muntari TBO ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa karar bindigan da mutanen kauyen suka ji ya sa suka fara arcewa a tunaninsu ‘yan bindiga ne suka kawo musu hari.

Ya ce daga baya an gano cewa ‘yan bindigan na harbi a sama saboda suna murnan cire sojoji daga wata makaranta da aka yi ne.

TBO ya ce kamata ya yi gwamnati ta sanar da mutane a kauyen kafin ta cire jami’an tsaro amma ba ta cire su ba a sani ba.

Daga nan wani mazaunin Jibia amma dan asalin kauyen Shimfida Bara’u Muhammad ya ce ya ga mata da yara kananan sama da 1000 da suka gudo daga Shimfida zuwa Jibia ranar Alhamis da yamma.

Muhammad ya ce mutane da dama da suka gudo daga Shimfida sun samu mafaka a Tashar Furera a makarantar firamare dake Jibia wasu ko sun nausa Jamhuriyar Niger ta kauyen Gurbin Baure.

Ya ce mutanen da suka guda daga Shimfida sun kako daga kauyen zuwa Jibia ta kafa.

Muhammad ya ce kansilan Shimfida da sauran mutane sun sun yi jana’izar yara bakwai da aka tattake suka mutu a Jibia sannan sauran mutanen da suka ji rauni na kwance a asibitin Jibia.

Wakilin PREMIUM TIMES ya yi kokarin tattaunawa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina Gambo Isa amma bai same shi ba a wayar Salula.