Gangamin APC na nan ranar 26 ga Maris, kuma Buni ne shugaban jam’iyya Daram-Dam – Ahmed

Shugaban Matasa na jam’iyyar APC Ismaeel Ahmed ya ce jam’iyyar ba ta karya dokar hukumar zabe ba wajen aikawa da ranar yin taron gangami na jam’iyyar.

INEC ta aika wa jam’iyyar wasiƙar cewa ba ta san da canjin shugabanci da aka yi a jam’iyyar ba saboda haka duk wani bukata da jam’iyyar ke nema daga wurinta tilas sai gwamnan Yobe Mai-Mala Buni ya saka sannu za su amince da ita.

Jam’iyyar APC ta aika wa hukumar zaɓe wasikar sanarwa da gayyatar ta taron kwamitin zartaswarta wanda za ta yi.

Sai dai kuma hukumar ta rubuta wa APC cewa ba za ta yi aiki da wannan wasika ba wanda gwamnan Neja ya saka wa hannu.

” Ba mu san da canjin shugaba a APC ba. Mala Buni muka sani shugaban jam’iyya na riko. Saboda haka idan ba hannun sa muka gani a takardar gayyatar ba da na sakataren jam’iyyar, toh babu ruwan mu da wannan gayyata.

Sai dai kuma ba kamar yadda gwamnan Kaf na ya ce ba wai Buhari ya basu daman su tsige Mala Buni su nada Sani Bello, jam’iyyar ta ce Buni da kan sa ya rubuta wasikar mika ragamar mulkin jam’iyyar ga gwamnan Neja, zuwa har sai ya dawo daga ganin likita a Dubai.

Wannan rudani dai ya sake jefa jam’iyyar APC cikin halin ƙaƙanikayi domin idan har bata iya tottoshe waɗannan ramuka ba wato barakar da jam’iyyar ta jefa kanta a ciki, babu yiwuwar za gudanar da taron gangami na jam’iyyar wanda za a yi ranar 25 ga wannan wata

Sannan kuma a jihohi da dama an samu rarrabuwan kai wajen zaɓen shugabannin jam’iyya da wasu har yanzu suna kotu.

Bisa ga waɗannan dalilai akwai yiwuwar zaben shugabannin jam’iyyar da za a yi ranar 26 ga wannan wata ba zai tabbata ba.

Martanin Ahmed

Ahmed ya sanarwa hukumar zabe cewa jam’iyyar bata karya dokar komai ba domin tun a watan Faburairu ta sanarw ahukumar INEC ranar da za ta yi gangaminta.

” Hakan kuma na nan daram-dam bai canja ba. Saboda haka hukumar ta kwantar da hankalinta babu abinda ya canja.

Sannan kuma game da maganan jagorancin jam’iyya da gwamnan Neja ya ke yi, ban ga abin rudani a ciki ba. Mala Buni ne shugaban jam’iyya na riko, idan baya nan gwamnan Neja ke rike masa har ya dawo. wannan ba sabon abu bane da wasu suka nemi zaucewa a kai. Mala buni shugaban APC na riko.