Gina Jami’oi masu zaman kansu zai sa dalibai samun guraben Karatu – Sarkin Kano, Aminu Bayero

Mai martaba Sarkin Kano Aminu Bayero yayi kira gaga attajiran kasar nan su tallafa wa fannin ilimi ta hanyar gina Jami’oi masu zaman kansu kamar yadda wasu masu hali ke yi a jihar Kano.
A cewar maimagana da yawun masarautar Kano, Abubakar Balarabe, sarkin yayi kiran ne a wajan taron Kaddamar da littafin tarihin rayuwar Shugaban rukunin kamfanonin AZMAN Abdulmunaf Sarina wanda aka yiwa lakabi da (RESILIENCE) aka kuma gudanar da taron a dakin taro na Jami’ar Bayero dake Kano.
Sarkin Bayero yace gina irin wadannan jami’oi masu zaman kansu a jihar Kano zai taimakawa dalibai su samu guraben karatu bayan kammala makarantun sakandire.
A don hakane ma ya yabawa Sarina bisa samar da wannan jami’a, yana mai cewa hakan zai cigaba da habbaka ilimi a jihar Kano, tareda godewa wadanda suke akan gaba wajan gina irin wadannan jami’oi masu zaman kansu.
Sarki Bayero yace a shekarun baya an samar da kamfanonin jiragen sama wadanda suka hada Kabo da Freedom da IRS air, inda yace yanzu kuma akwai Azman da Rano air, kuma dukkaninsu kamfanonin jirage ne na “yan asalin jihar Kano.
Sarki Bayero daga bisani yayi Kira ga al’umma su ci gaba da jajircewa wajan yiwa Najeriya addu’oin samun zaman lafiya da hadin kan al’ummar wannan kasa, ya kuma yi addu’ar zabuka masu zuwa Allah yasa ayi su lafiya a gama lafiya tareda zaba mana shugabanni nagari.