AMAI DA GUDAWA: An samu karuwa a yawan mutanen da cutar ta kashe daga 20 zuwa 51

An samu karuwa a yawan mutanen da cutar kwalara ta kashe a Ekureku dake karamar hukumar Abia jihar Cross Rivers daga mutum 20 ranar Asabar zuwa mutum 51 ranar Litini.

Shugaban garin Ekureku Bernard Egbe ya sanar da haka ranar lokacin da dan takaran kujeran gwamnan jihar a karkashin jami’yyan PDP Sandy Onor ya kawo wa kauyen ziyara.

Egbe wanda ya koka da yadda cutar ke yaduwa ya ce wadanda suka kamu da cutar na kwance a asibitin dake kauyen likitoci na basu magani.

Ya ce cutar ta bullo ranar Alhamis a kauyuka 10 dake Ekureku sannan tun daga lokacin yankin ke samun tallafi daga UNICEF, WHO da ma’aikatan gwamnati.

Dan takaran kujeran gwamnan jihar a karkashin inuwar jami’yyar PDP Onor ya tausaya wa mazaunan Ekureku sannan ya tabbatar cewa idan har ya zama gwamna zai Samar wa yankin tsaftacen ruwan sha.

Idan ba a manta ba a ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban hukumar cibiyar kiwon lafiya na matakin farko ta jihar Janet Ekpeyong ta bayyana cewa gwamnati ta dauki tsauraran matakan da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar.

Janet ta ce gwamnati ta aiko da magunguna da kwararrun ma’aikatan domin dakile yaduwar cutar.

Bayan haka babban sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar Iwara Iwara ya ce cutar ta kara bullowar a wani kauye dake karamar hukumar Odukpani dake jihar.

Ya ce tuni gwamnati ta aiko da magunguna da ma’aikata domin hana yaduwar cutar a kauyen.