Gaskiya ban gamsu da matsayin tattalin arzikin Najeriya ba – Buhari

A karon farko bayan shekaru shida a kan mulki, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana rashin gamsuwar sa da yanayin tattalin arzikin Najeriya.

Buhari ya bayyana haka a wata tattaunawa da Gidan Talbijin na Kasa, NTA ya yi da shi a ranar Alhamis da dare.

Shugaba Buhari ya ce a gaskiya ya yi matukar damuwa da halin da tattalin arzikin Najeriya ya shiga.

Sai dai kuma ya ƙara shan alwashin cewa gwamnatin sa za ta tayar da komaɗar da tattalin arzikin Najeriya ya samu sakamakon kutufo ɗin da ya sha daga matsaloli da ƙalubale daban-daban.

“Gaskiya ban gamsu da tattalin arzikin Najeriya ba.” Haka Buhari ya bayyana matsayin amsar tambayar da aka yi masa kan tattalin arzikin Najeriya.

Sai dai kuma ya ce gwamnatin sa na ƙoƙarin ganin baƙi na ƙara zuba jari cikin ƙasar nan daga ƙasashen waje.

Buhari wanda ya hau mulki cikin 2015 bisa alƙawarin kawar da rashawa da cin hanci, matsalar tsaro da kuma inganta tattalin arzikin ƙasa, a yanzu kuma bayan shekaru shida ya gamsu da cewa har yau tattalin arzikin Najeriya ki dai tafiyar-kura ya ke yi, ko kuma tsalle ya ke ta yi, ba gudu ba.

Haka a ranar Juma’a cikin wata tattaunawa da ya yi da Gidan Talbijin na Arise TV, Buhari ya bayyana cewa “daƙile cin hanci da rashawa a ƙarƙashin gwamnatin dimokuraɗiyya, abu ne mai matuƙar wahala.”

PREMIUM TIMES ta buga sharhin yadda Buhari ya shafe shekaru shida kan mulki, amma ya kasa samun nasara a shika-shikan tattalin arzikin ƙasa guda bakwai.

Buhari ya ƙara haifar da tsadar rayuwa maimakon a samu sauƙi, farashin kayan abinci da na kayan masarufi a kullum sai tashi sama su ke yi. Ga matsalar taɓarɓarewar darajar Naira, ga rashin aikin yi ga kuma rashin bunƙasar noma, duk kuwa da ɗimbin biliyoyin nairorin da ake bayarwa ramce ga manoma.