An dakatad da Sarkin Zurmi a jihar Zamfara

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Mai girma gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle, ya dakatar da Sarkin Zurmi, Alhaji Atiku Abubakar Muhammad tare da baiwa Alhaji Bello Sulaiman (Bunun Kanwa) damar gudanar da ragamar masarautar na riƙon ƙwarya.

A cikin wata sanarwa da muƙaddashin sakataren gwamnatin jihar Kabiru Balarabe ya fitar a ranar Juma’a, gwamnan ya dakatar da Sarkin ne bisa zarginsa da hannu a ƙaruwan hare-haren ƴan bindiga a yankin masarautar Zurmi.

Sanarwar ta ce tuni Gwamna Bello Matawalle ya naɗa kwamitin mutum Tara (9) ƙarƙashin jagirancin tsohon mataimakin gwamnan jihar Malam Ibrahim Wakkala Muhammad domin gudanar da bincike kan zargin da ake yi akan dakataccen Sarkin.

An baiwa kwamitin makwanni uku su gabatar da sakamkon binciken nasu.