HAJJI 2021: Korona ta sake sa kasar Saudiyya ta hana aikin Hajji ga kasashen duniya bana

Kasar Saudiyya ta bayyana cewa babu wani maniyyaci da zai je aikin Hajjin 2021 na bana, saboda kauce wa yaɗuwar cutar korona.

Sanarwar dai na nufin babu maniyyaci ko ɗaya da za a bari ya shiga daga Najeriya da sauran ƙasashe.

Jaridar Arab News, Saudi Gazzete da wasu jaridun Najeriya sun ruwaito cewa mahukuntan ƙasar sun ce mutum 60,000 ɗin da a watan jiya aka amince za su yi aikin Hajjin 2021, za su kasance duk ‘yan ƙasar Saudiyya ne, sai kuma ‘yan sauran ƙasashe da ke zaune a cikin ƙasar Saudiyya ɗin.

Wannan sabon hukunci da Saudiyya ta kafa, ya shafe sanarwar farko wadda ƙasar ta gindaya sharuɗɗan da maniyyaci daga ƙasashen waje za su cika kafin su shiga ƙasar Saudiyya aikin Hajjin bana.

Za a fara aikin Hajji a tsakiyar watan Yuli, inda a karo na biyu ma aka hana ƙasashen waje halarta, bayan hana su da aka yi a 2020.

Tsohuwar Dokar Shiga Saudiyya Aikin Hajji, Kafin Hana Kasashe Shiga:

Kasar Saudiyya ta gindiya sharudda guda 10 tsaurara wajen gudanar da ayyukan Hajjin bana na 2021.

Daga cikin sharuddan dai an hana dattawa masu shekaru 61 zuwa sama zuwa aikin Hajji, kuma an hana kananan yaran da ba su kai shekaru 18 a duniya ba.

Saudiyya ta kuma ce gaba daya mutum 60,000 ne za su gudanar da aikin Hajjin bana. Kuma za su kasance a cikin su din ma akwai ‘yan kasar Saudiyya.

Kafin bullar korona dai akan samu mahajjata har miliyan 2.5 ko sama da haka a lokaci guda.

Sharuddan Da Saudiyya Ta Gindaya A Hajjin 2021 Kafin Ta Hana Ƙasashe Zuwa:

1. Musulmai 60,000 KADAI za su yi aikin Hajjin 2021, wadanda sun kunshi ‘yan asalin kasar Saudiyya da sauran daga kasashe daban-daban.

2. TILAS sai wanda ya kai shekaru 18 zuwa shekaru 60 za a bari ya yi aikin Hajjin 2021.

3. Kuma TILAS sai maniyyaci ya na da cikakkar lafiya.

4. Kuma TILAS sai maniyyaci ya nuna shaidar cewa watanni shida kafin aikin Hajji ba a kwantar da shi asibiti ba, kuma bai je asibiti ganin likita dangane da wata lalura ba.

5. TILAS ya kasance maniyyaci na dauke da katin shaidar an yi masa allurai biyu na rigakafin cutar korona. Zai bayar da katin shaida daga Ma’aikatar Lafiya ta kasar sa ko asibitin da aka yi masa rigakafin.

6. TILAS ya kasance samfurin allurar rigakafin da aka yi wa maniyyaci ta kasance irin wadda Ma’aikatar Lafiya ta Saudi Arabiya ta yarda da ingancin ta ce.

7. TILAS duk maniyyacin da ya isa Saudiyya daga wata kasa, sai an fara killace shi tsawon kwanaki uku tukunna kafin ya wuce Makkah ko Madina.

8. TILAS allurar rigakafin korona da aka yi wa mutum, ta kasance an yi ta farkon zuwa ranar 1 Ga Shawwal, 1442 (zuwa ranar Karamar Sallah kenan).

9. TILAS ya kasance allurar rigakafin korona ta biyu da aka yi wa maniyyaci, an yi ta kwanaki 14 kafin isar sa kasar Saudi Arabiya.

10. TILAS za a rika tsaurara matakan kare kai ko kare bazuwar cutar korona a lokacin aikin Hajji. Matakan da su ka hada da: Yin nesa-nesa da juna da bayar da tazara tsakanin mutum da mutum, saura takunkumin baki da hanci da sauran matakan da aka wajabta a kiyaye don kare rayuka da lafiyar mahajjata.