Gasar Kofin Duniya Ta Mata: Tinubu Ya Mika Sakon Fatan Alheri Ga Tawagar Super Falcons

Shugaba Ahmed Bola Tinubu ya mika sakon fatan alheri ga ‘yan wasan kwallon Najeriya na Super Falcons yayin da suke shirye-shiryen karawa da Australia a wasansu na biyu na rukuni a gasar cin kofin duniya ta mata na FIFA da ke gudana a Australia da New Zealand 2023.