Zulum ya bada odar a murkushe ‘yan kungiyar ‘ƴan Iska’ da ake kira ‘Marlians’ da su ka addabi mutanen Maiduguri

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya umurci jami’an tsaro a jihar da su murkushe ayyukan kungiyar ‘yan ta’adda da ke kiran kansu ‘Marlians’.
Ana zargin kungiyar da muzguna wa mutanen jihar.
Mafi yawa daga cikin ƴan kungiyar matasa ne. Suna aikata ayyukan ta’addancin su ne a babban birnin jihar, Maiduguri, da Jere, wani gari dake kusa.
Gwamnan a wani taron gaggawa na tsaro da ya gudanar kan barazanar kungiyar a ranar Laraba, ya ce dole ne a murkushe kungiyar nan take.
Mazauna garin Maiduguri dai na zargin kungiyar da yi wa mutane fashi, kwace, sata, fyade, harkallar muggan kwayoyi da dai sauransu. Sannan ana kuma zargin ƴan kungiyar da kai hari tare da kashe jami’an tsaro a jihar.
“Na kira wannan taron majalisar tsaro na gaggawa ne domin magance matsalar tsaro da ke addabar babban birnin Maiduguri da wasu sassan karamar hukumar Jere.
Sai dai kuma bayan wannan ganawa, rundunar tsaron jihar sun kai samame wasu unguwanni a garin n na Maiduguri inda suka yi gagarimin kame har mutum 78. Ciki har da wani kasurgumin ɗan iska da ake nema ruwa a jallo.
Unguwanni da jami’an tsaro suka kai wa hari sun hada da Abuja Sheraton, Njimtilo, Bayan Quarters, Galadima, Kasuwan Shanu, Santiago, Bayan Texaco, Koren Tanki, Tashan Bama, London Ciki, Tudun Wada, Tashan Kano, da Borno Express.
Su dai ‘Marlians’ ba su bar komai da kowa ba, sune fasa shaguna, kwashe, shaye-shaye, fashi, fyade, fade-fade da sare-sare da dai sauransu.