Dalilin da ya sa kungiyar Likitoci NARD, ta tsundima yajin aiki

Kungiyar likitoci NARD, ta fara yajin aikin ‘Sai baba ta gani ‘ ranar Laraba

Shugaban kungiyar Emeka Orji ya sanar da haka a daren Talata.

Wannan sanarwar ya zo ne bayan zaman da kungiyar ta yi da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abass.

Ƙorafin kungiyar:

Kungiyar NARD ta yanke shawarar fara yajin aiki bayan zaman da kwamitin zantarwar ta yi a Yuli a jihar Legas.

Idan ba a manta ba a ranar 17 ga Mayu ne kungiyar ta fara yajin aiki kwanaki biyar domin bai wa gwamnati dama da tunatar da ita alkawuran da ke tsakanin da da su.

Kungiyar na neman gwamnati ta cika alkawuran da ta ɗauka a baya na biya wa likitocin ƙasar nan buƙatunta.

Bukatun sun haɗa da ɗaukan sabbin likitoci domin maye gurbin waɗanda suka fice daga kasar nan. Sannan kuma da biyan kuɗaɗe alawus da dama da suke bin gwamnatocin baya.