RUFE ƘOFA DA ƁARAWO: Buhari ya yafe wa Dariye, Nyame laifin satar kuɗin talakawa, ya yi wa wasu 157 afuwa

Majalisar Zartaswa ƙarƙashin ikon Shugaba Muhammadu Buhari ta yafe wa tsohon Gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye da tsohon Gwamnan Taraba, Jolly Nyame, waɗanda yanzu haka ke ɗaure a kurkuku, bayan yanke musu hukuncin satar maƙudan kuɗaɗen talakawan jihohin su.
Gwamnonin biyu a cikin mutum 159 da aka yafe wa laifukan da su ka aikata, a taron da Majalisar Zartaswar ta yi ranar Alhamis a Fadar Shugaban Ƙasa.
Daga cikin sauran waɗanda aka yafe wa ɗin, akwai tsohon janar kuma Minista a zamanin mulkin Abacha, Tajudeen Olariwaju, Kanar Akiyode, tsohon hadinin Mataimakin Abacha, watau Janar Oladipo diya da sauran dukkan jami’an sojojin da aka ɗaure waɗanda aka kama da laifin yunƙurin juyin mulkin Gideon Orkar, cikin 1990.
Majiya daga Fadar Shugaban Ƙasa ta ce an yafe wa Dariye da Nyame ne bisa dalillai na rashin lafiya da kuma tsufa.
Shekarun Nyame 66, ya yi Gwamnan Jihar Taraba daga 1999 zuwa 2007. An ɗaure shi shekaru 12 a kurkukun Kuje. A cikin 2020 ne Kotun Koli ta jaddada amincewa da ɗaure shi.
Shi kuma Dariye shekarun sa 64. Ya yi Gwamnan Filato daga 1999 zuwa 2007, ya na kurkuku ne saboda satar Naira biliyan 2. An ɗaure shi ya na sanata cikin 2018. Amma bai tafi kurkuku ba har sai da ya kammala wa’adin sa cikin 2019.
Da farko kotu ta ɗaure shi shekaru 14, amma Kotun Ƙoli ta maida hukuncin shekaru 10.
Taron Majalisar Ƙoli dai ya samu halartar dukkan tsoffin shugabannin Najeriya da ke raye, in bada Olusegun Obasanjo, wanda a yanzu haka ke Amurka ana duba lafiyar su.
Su Wane Mambobin Majalisar Ƙoli:
1. Shugaban Ƙasa (shugaban majalisa).
2. Mataimakin Shugaban Ƙasa (mataimakin shugaban majalisa).
3. Dukkan tsoffin shugabannin Najeriya na dimokraɗiyya da na soja.
4. Dukkan tsoffin Shugabannin Kotunan Najeriya.
5. Shugaban Majalisar Dattawa.
6. Kakakin Majalisar Tarayya.
7. Dukkan gwamnoni masu mulki a yanzu.
8. Antoni Janar na Tarayya, Ministan Shari’a na yanzu.