FARMAKIN GIDAN KASON JOS: Mutum 10 sun mutu, 252 sun arce

Hukumar NCoS ta bayyana cewa mutum 10 sun mutu sannan fursinoni 252 sun gudu sandiyyar harin da ‘yan bindiga suka kai gidan Kason Jos jihar Filato.
Kakakin hukumar Francis Enobore ya sanar da haka ranar Litini a Abuja.
Enoboreya ya ce daga cikin mutum 10 din da suka mutu akwai ma’aikacin hukumar daya sauran kuma duk fursinoni ne da suka nemi gudu ta ritsa da su.
Sannan akwai mutum 6 da suka ji rauni a dalilin harin.
Ya ce hukumar ta kama mutum 10 daga cikin wadanda suka gudu kuma har yanzu ana farautar saura fursinoni 252 da suka gudu.
Ya yi wa iyalin ma’aikacin hukumar ta’aziya sannan ya jinjina wa jami’an tsaron da suka taimaka wajen kama maharan da suka kawo hari a wannan gidan yari.
Enoboreya ya tabbatar cewa hukumar za ta kama duk wadanda ke da hannu a harin domin yanke musu hukunci.
Idan ba a manta ba a ranar Lahadi PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda ‘yan bindiga suka kai farmaki gidan yarin garin Jos da misalin karfe 5:30 na yamma.
‘Yan bindigan sun yi batakashi da ma’aikatan NCoS kafin suka samu daman shiga cikin gidan yarin.
Sai dai Enoboreya ya ce ‘yan bindigan sun makale a cikin ginin gidan kason saboda tare wurin da jami’an tsaro suka yi.
Gidan yarin Jos na da fursinoni 1,060 inda a ciki akwai fursinoni 560 dake jiran a yanke musu hukunci da kuma wasu fursinoni 500 da aka yanke wa hukunci suna jira akaddamar da hukuncin ne.