TAMBUWAL YA TAKA RAWAR GANI: Za a kaddamar da sabon asibitin da babu kamar a Sokoto

Gwamnatin jihar Sokoto ta kammala gina katafaren asibitin gwaje-gwaje sannan har tana Shirin kadamsr da ginin ranar Laraba mai zuwa.

Gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa tare da gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal, manyan jami’an gwamnati da kungiyar likitocin Najeriya NMA za su halarci bukin bude wannan katafaren asibiti a garin Sokoto.

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Mohammad Ali Inname ya bayyana cewa asibitin za ta samar wa mutane a ciki da wajen kasar nan ingantaccen kiwon lafiya da gwaje gwaje da ake samu a manyan kasashen waje.

Inname ya ce an fara daukan ma’aikatan da za su yi aiki a asibitin.

Ya ce kamfanin ‘Healthfield Medical Services Ltd’ ne za ta kula da asibitin amma a karkashin tsarin da gwamnati yi na hadin guiwa.

An kashe Naira biliyan 3.2 wajen gina asibitin da kuma saka kayan aiki a ciki.

Kamfanin ‘Katuru & Partners Limited’ ce ta ta yi kwangilan gina asibitin sannan kamfanin ‘Minjiriya Medical Services Limited’ ta yi kwangilar zuba ingantattun kayan aiki na zamani a cikin sa.

Sakamakon bincike ya nuna cewa duk shekara ‘yan Najeriya sama da 5,000 na fita zuwa kasashen waje domin neman ganin likitoci da asibiti

A dalilin hakan ya sa Najeriya ke asarar sama da dala biliyan daya duk shekara.