Fargaba ta sa an rufe katafaren rukunin shagunan Jabi Lake da ke Abuja

An rufe fitaccen rukunin shagunan sayayyan nan na Jabi Lake da ke babban birnin tarayya Najeriya Abuja.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da fargabar rashin tsaro na yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a birnin.

A ƙarshen makon da ya wuce ne Amurka ta fitar da gargadin cewa akwai yiwuwar za a kai hare-haren ta’addanci a fadin Najeriya, musamman ma Abuja, lamarin da ya ɗaga hankulan jama’a.

Fargaba ta ƙaru matuka, bayan da ofisoshin jakadancin wasu ƙasashen da ke Abujan suka gargadi jama’arsu da su yi taka tsantsan don fargabar abin da ka iya faruwa, BBC ta ruwaito.

A wata sanarwa da hukumar rukunin shagunan ta fitar, ta bai wa masu hulɗa da su haƙuri kan duk wani abu da ba su ji dadinsa ba sakamakon matakin.

  • Fargaba ta sa an rufe katafaren rukunin shagunan Jabi Lake da ke Abuja
  • Ɗan Chinan nan da ake zargi da kashe tsohuwar budurwarsa a Kano ya musanta
  • CBN zai sauya fasalin wasu takardun kudin Najeriya

“Muna bai wa jama’a haƙuri cewa za mu rufe rukunin shagunan a yau Alhamis 27 ga watan Oktoban 2022.

“Mun ɗauki matakin ne don kare al’umma da kuma ma’aikatan wajen,” in ji sanarwar,

The post Fargaba ta sa an rufe katafaren rukunin shagunan Jabi Lake da ke Abuja appeared first on Hausa Daily Times.