FIGC Ta Bukaci Takardun Binciken Aikata Magudi Kan Juventus Da Aka Kammala

Hukumar kwallon kafar Italiya (FIGC) ta bukaci masu bicike a garin Turin su zakulo sabbin takardun binciken da suka kammala a kan kungiyar Juventus mai wasa a lig din Serie A, da ake zargi da tafka magudi a kasuwar hada hadar ‘yan wasa a cewar wata majiya makusanciya da batun.