Dole mu yi amfani da ikon mulki domin kawo ƙarshen matsalar tsaro,- Buhari ga Ƴan Majalisa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace Gwamnatin sa a shirye take tayi amfani da duk abinda ya dace karkashin ikon ta don kawo karshen rashin tsaro a kasa, dama zakulo masu kitsa aikata miyagun aiyuka.

Shugaban kasa, wanda yayi wannan magana ranar Talata yayin liyafa da membobin Majalisar Kasa, daya gudana a babban dakin taro na Fadar Gwamnati Abuja, yace, “Rashin Tsaro da ya hada da aiyukan tada ƙayan baya, Ɓarayin daji, yin garkuwa da Mutane da sauran aiyukan ta’addanci shine matsala daya tilo da yanzu muke fuskanta.”
A wani jawabi da mai baiwa shugaban kasa shawara a fannin harkokin yada Labarai Femi Adesina ya fitar, shi kuwa Hadimin shugaban kasa Buhari Sallau ya fassara, ya ce shugaban ya bayyana damuwar cewa rashin tsaro ya kawo cikas wa kokarin Gwamnati na gina Manyan aiyuka, da samar da abinda akafi bukata na more rayuwa ga mutane, da jawo hankali masu zuba jari wanda zasu jagoranci kawo Sabbin abubuwan sauye sauye, da kirkiro da Masana’abtu da samar da aiyukan da zai kawo arziki.
“Wasu cikin mutanen dake kitsa wadan nan rashin tsaro sunayin Hakane don wata riba, wasu ko da sunan batanci ga Tsarin da ake kai.” koma menene abinda ka iya kwadaitar dasu, abinda suke aikatawa barazana ce ga wanzuwar Kasar mu.” A wannan yanayin, dole muyi duk abinda ya dace karkashin ikon dake akwai garemu, batare da la’akari da ƙauda hankula ba, mu kawo karshen aiyukan su da zakulo masu aikata laifukan.” Bazamu bari a ƙauda hankalin su akan wannan abinda mukasa gaba ba, ko raunana akan zagewar mu, kuma inada Ƙwarin gwiwa cewa a tare zamuyi nasara cikin kokarin da muke yi,” Cewar Shugaban.
Shugaba Buhari ya kuma yi amfani da wannan dama Gurin jinjina ga Majalisa ta tara 9 bisa kan yadda suke aikatar da aikin su cikin Dattako da kwarewa, ya bayyana Majalisar a Matsayin” Abokan tafiya Gurin cigaban Ƙasa.”Shugaban ya yaba musamman Jam’iyu marasa rinjaye a majalisa kan hadin kai da goyon baya aiyukan Gwamnati“Damar da muke da ita na mulki ta yadda Ƴan Najeriya ke bukata ya rataya kan Muhimmin hadin kai mai Imfani da taimakekeniya tsakanin Bangaren Majalisa data Mulki.“Hakkin bincike da daidaita kan dukkanin mu abune daya zamo wajibi a samu rashin daidaito, kuma hakan bazai zamo dalilin jayayya da sabanin Ra’ayi ba matukar akwai tuntuban juna, Alkaleri da samun Jayayya sau tari yana nuni kan Shine abu dazai sanya a samu tuntuban juna yadda ya dace.
“A Majalisa ta Tara 9, kun mutunta kawunan ku ta hanyar nuna halayya mai kyau a ofis, ta yadda ma’aunin ya nuna kyawun yadda kuke aiwatar da aikin ku, dama kuma nuna kwarewa gurin tunkarar tambayoyi mai wahala dake fuskantar Kasar nan cikin Mutunta ka da gogewa,” Cewar Shugaban.Shugaban ya zayyano wasu cikin nasarori da majalisa ta tara ta Cimma farawa daga Nasarar Maida Tsarin Kasafin kudin kasa daga watan Janeru zuwa Disamba, Sabunta dokar Companies and Allied Matters Act (CAMA), da Dokar Hukumar Ƴan sanda ta kasa, da Dokar Kudi, da dai Sauran su da dama.Da yake yaba Shugabannin Na Majalisar Karkashin Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da Kakakin Majalisar Dokoki na kasa Femi Gbajabiamila, bisa irin sa daukarwan har zuwa lokacin da Ƙasar ke cikin kalubalen, Shugaban ya fadi wa Ƴan Majalisun“Kun kuma yi Nasarar shawo kan kalubalen Siyasa da Sauran kalubale dake akwai, na tsawon lokaci, da kuma kawo gyaran dokar da aketa hankoro na Kamfanonin  Mai da Iskar Gas, wanda yanzu hakan ya kawo Nasarar amincewa da dokar Petroleum Industry Bill (PIB).
“Ina taya ku Murna dukka, kuma ina Godiya kan irin Gudumowa da kuke bayarwa a mawuyacin hali, kan abubuwa da suka wajabta don gina kasa.”Shugaban kasa ya lura cewa Bangaren Mulki da Majalisa sun fara aiki ne a wani lokaci da Ƙasar ke fama da Kalubale masu tarin yawa.
“Shawo kan wadan nan kalubalen yana bukatar cewa mu kawo karshen Matsalar dake addaban mu kuma akayi watsi dashi na tsawon lokaci na Tattalin arziki, Siyasa, doka da tarihi wanda sau da dama sune tushen Matsalolin da Kasa ke ciki.“A irin wannan lokaci cikin Tarihi ya bukatar muyi zabi mai tsauri, Mu dauki matakai masu wahala da yin aiki cikin gogewa da Ƙishin Kasa don tabbatar da cewa Kasar mu zata iya tsira da bunƙasa nan gaba bayan mun tafi.“Abin da haka ke nufi Shine aikin mu bazamu sameshi cikin sauki ba, sai de duk da haka, abinda muka sa gaba mukeson cimma, zamuyi aiki tare da juna don samun Nasarar sa, hakan ya dace da kokarin ba kuma tare da yin la’akari da sadaukarwar mu ba,” Inji shi.
A dai dai lokacin da shekara na biyu na Majalisa ta Tara yazo karshe, shugaban kasa ya lura cewa ya dace ya sake haduwa dasu don yin dubi da tattauna wa kan  aiyukan, don gano abubuwa da akayi nasarar cimmu su, da wa’anda har yanzu ba’a kai ga nasara ba.
“Ta wannan hanya ce, zamu iya bada fifiko kan aiyukan da gano inda ya wajabta mu samar da Kudade don tabbatar da cewa a lokacin wannan Majalisa, da wannan Gwamnati, Mun samu dama na kammala aiyukan da muka fara, da barin tarihi na nasarori wanda zai kafu Baza’a mance damu ba dukka cikin Tarihi,”Shugaban kasa yace yana zuba ido don Cigaban samun hadin kai da aiki tare da juna tsakanin bangaren Mulki dana Majalisa, aiki tare don cimma nasara da hankoron samun kasa mai zama lafiya da yalwan Arziki.