TARZOMA NA NEMAN GURGUNTA AFRIKA TA KUDU: An kashe mutum 72, an wawashe ‘Super Market’ sama da 600 cikin kwana biyu

Tarzomar da ta ɓarke a Afrika ta Kudu ta yi munin da a cikin kwanaki biyu an kashe mutum 72.

Tarzomar ta ɓarke bayan da Babbar Kotun ƙasar ta ɗaure tsohon Shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma watanni 15 a kurkuku, saboda ya bijire wa umarnin gayyatar kotu.

An tsare shi a ranar 7 Ga Yuli, 2021, kuma PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin zargin cin hanci da rashawa da harƙallar kwangilolin da ake yi wa Zuma.

‘Yan Sandan Afrika ta Kudu sun ce adadin waɗanda su ka mutu ɗin ya zuwa ranar Talata, su 72, yawanci tattake su aka yi wurin tirmitsitsin kwasar kayayyaki a manyan kantinan ƙasar.

Sun ce zuwa yammacin Talata an safa ‘super market’ fiye da 600, an yi masu ƙarƙaf.

“Kayan da aka lalata a birnin Johannesburg da manyan garuruwa sun kai na biliyoyin rand, kuɗin ƙasar.

Mahukuntan sun ce an kama mutum 1,234 yayin da aka tantance wasu gaggan mutum 12 da ‘yan sanda ke zargin su ne su ka ruruta tarzomar.

Tun da farko dai lauyan Zuma ya ce bai kamata a ɗaure shi ba. Yayin da kotun ta ce za ta duba lamarin nan gaba.

Har yau dai a ba sa ranar duba lamarin ba.

Hukumar Kula da Kayan Masarufi ta Afrika ta Kudu ta yi kira ga Shugaba Ceril Ramaposa ya ƙaƙaba dokar-ta-ɓaci, saboda ana ci gaba da kwasar kayayyaki a yawancin manyan biranen ƙasar.