EFCC ta samar da manhajar da za ta taimaka wajen tona asirin ƴan rashawa

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ‘EFCC’, ta ƙaddamar da wata manhaja da za a yi amfani da ita domin al’umma su dauki hotunan abubuwa ko wuraren da ake aikata laifuka.

Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa, wanda shi ya jagoranci ƙaddamar da manhajar mai suna ‘Eagle Eye’ wato Idon Mikiya a Abuja a yau Laraba, ya bayyana wa manema labarai yadda ake sauketa a waya.

Abdulrasheed Bawa ya ce yunƙurin nasu yana cikin shirin nan na kwarmata bayanai da ake Whistle Blower a Ingilishi.

“Duk wanda yake so ya kwarmata mata bayanai don ya samu wani abu zai iya yin hakan a ciki kuma ya bayyana cewa ya yi hakan ne a matsayinsa na mai kwarmata bayanai,” a cewarsa.

Ya ƙara da cewa mutum zai iya ɗaukar hoton gidan da ake aikata laifin rashawa da kuma adireshinsa ya turo musu, “mu kuma sai mu bincika”.

Domin sanin yadda ake sauke manhajar a wayoyin salula, ya ce ana iya samun manhajar a App Store ga masu wayoyin Apple da kuma Google Play Store ga masu amfani da Android.

“Idan aka sauke ta za ta yi aiki ne kamar yadda Facebook ko WhatsApp yake a waya. Duk lokacin da kake son yin amfani da ita za ka buɗe ne kawai ka fara.

“Mutum zai iya ɗaukar hoton gidan (da ake aikata laifin rashawa) da kuma adireshinsa ya turo mana mu kuma sai mu bincika. Idan ya ga dama ya faɗa mana sunansa, idan bai ga dama ba kuma shikenan.”

Sai dai majiyarmu ta BBC ta ce shugaban ya gargaɗi masu kwarmata bayanai cewa dole ne su tabbata cewa bayanan da za su bayar na gaskiya ne.

“Idan mutum ya faɗa mana bayanai za mu gayyace shi ya zo ya cike wasu takardu sannan kafin a fara za mu faɗa masa cewa idan muka gano bayanan nasa ƙarya ne, yana yi ne don tozarta wani, to shi ma fa hannun doka zai kama shi,” in ji shi.