DOKAR HANA GARARAMBA DA SHANU: Gwamnatin Bayelsa ta kwace wa Fulani shanu 34

Kwamitin Hana Makiyaya Gararambar Kiwo na Jihar Bayelsa (BSLMC), ta kama shanun makiyaya 34 a Yenagoa, saboda karya dokar hana kiwo.

Cikin watan Maris ne Gwamnatin Jihar Bayelsa ta kafa dokar hana yawon gararambar kiwon shanu a jihar.

An kwace shanun ne saboda an same su su na kiwo a Rukunin Gidajen Gandun Noman Kwakwar Man Ja a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Shugaban Kwamitin BSLMC, David Alagoa, ya ce makiyayan da su ka mallaki shanun sun kora shanun sun shiga cikin gonakin tsakar dare domin su yi kiwo lokacin da mutane ke barci.

Alagoa wanda kuma shi ne Kwamishinan Ayyukan Noma, ya ce zai amfani da abin da dokar haramta kiwo a Bayelsa ta tanadar.

‘Ba Za Mu Saki Shanun Ba Sai An Biya Kudin Tara’ -Kwamishina:

Kwamishinan Gona na Jihar Bayelsa Dvid Alagoa ya ce ba za a saki shanun da aka kama wa makiyayan ba, har sai sun biya kudin tara, kamar yadda doka ta tanadar.

“Mun dade mu ka kiwon hankalin su, tare da sa ido kan irin barnar da su ke yi. Har dai a wannan karo mu ka ba su mamaki.”

Ya ce kwamitin sa na aiki tare da sauran kananan hukumomi domin tabbatar da cewa kowace karamar hukuma ta tsaurara dokar haramta kiwon.

An kuma bada umarnin duk inda aka ga shanu na gagaramba, to a sanar da kwamiti kai-tsaye.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Bayelsa Aminu Alhassan ya ce ana nan ana wayar da kan jama’a kafin dokar ta fara aiki gadan-gadan.