Ƙungiyar Matasan Arewa ta yaba kan dakatar da kafar Twitter a Najeriya

Ƙungiyar matasa ta Arewa maso gabas da a kafi sani da suna Movement of North east Youth Organisation Forum a turance, ta yabawa gwamnatin tarayya kan matakin dakatar da kafar sadarwa ta Twitter a ƙasar nan, kan zargin yaɗa tashin hankali da ta ke yi.

Shugaban ƙngiyar Alhaji Abdurrahman Buba Kwaccham wanda ya bayyana hakan a yayin zantawa da ’yan jarida a ranar Alhamis a Abuja, ya buƙaci gwamnatin da ta jajirce a kan matakin, har sai kamfanin ya cika sharuɗan ƙasar nan kan almuranta na tsaro.
Ƙungiyar matasan ta bayyana gamsuwarta kan matakin janye wani sashi na bayanin tsawatawa da kafar ta yi daga cikin jawabin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan masu kai hare-hare ga jami’an tsaro da kuma cibiyoyinsu a yankin jihohin Kudu maso gabas, a yayin da a gefe guda a ke barin waɗanda a ke zargi da kai harin, na cin karensu babu babbaka, ba tare da yi masu shinge ba, kamar yadda ta yi zargi.
Alhaji Abdurahman Buba Kwaccham ya kuma bayyana marhabin da sanarwan da Ministan yaɗa labarai Alhaji Lai Muhammad ya yi a ranar Laraba na fara yi wa kafofin sada zumunta irinsu Facebook da Twitter da kuma Instagram rajista, gabanin iya yaɗa al’amuransu a sararin samaniyar Najeriya, wanda ya ce abin a yaba ne.
Ya yi misali da tarar dala miliyan 267 da ƙasar Faransa ta yi wa kamfanin yanar gizo na Goggle a ƙasar, inda ya ce barin abubuwa kara zube shi ne ya ke basu damar cin karensu babu babbaka a ƙasashen Afrika da a wani zubin ke jawo tashin hankali, inji shi.
“Akwai lokacin da a ka rufe xaukacin kamfanonin sadarwa a jihohi 3 na yankin arewa maso gabar da ke qarqashin dokar ta vaci da gwamnatin baya ta yi don samar da tsaro, wanda kuma hakan ya yi tasiri.
“To ina mamakin yadda wasu a yanzu ke ƙorafin cewa dakatar da kamfanin na Twitter take ’yancin faɗan albarkacin baki ne, duk da barazanar da hakan ke iya yi ga bangaren tsaro”. Inji Kwacham.
Shugaban matasan ya ce “akwai kamar ƙasashe bakwai da su ka rufe kafar ɗungurugum a ƙasashensu, alhali matakin da Najeriya ta ɗauka na wacingadi ne kawai”.