Dan majalisar dokoki na jihar Kano ya doka ‘Ribas’ bayan ya tsunduma lambun jam’iyyar NNPP, ya ya rungumi tsintsiyar sa ya dawo APC

Dan majalisan dokoki dake wakiltar Bagwai/Shanono a jihar Kano Ali Isah ya doka ‘Ribas’ bayan har ya tsunduma lambun jami’yya mai alamar kayan daɗi NNPP, ya dawo APC ya rumgumi tsintsiyar sa.
Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda ‘yan majalisan dokokin jihar Kano 9 suka canja sheka daga jami’iyyar PDP zuwa Jami’iyyar NNPP a cikin makon jiya.
Isah wanda ɗan jami’iyyar APC ne ya koma jami’iyyar NNPP, bayan ‘yan kwanaki sai kuma ya ji kamar ayabar ce ko kankanar ce bata yi masa ba a alambur sai ya dawo APC ya rungumi tsintsiyar sa.
Kakakin majalisar Uba Abdullahi ya sanar da haka yana mai cewa Isah ya bayyana dawowarsa jami’yyar APC a wasikar da ya aika wa majalisar dake dauke da kwanakin wata 17 ga Mayu.
A wasikar Isah ya ce a shirye yake ya hada hannu da jami’yyar domin ganin jami’yyar ta yi nasara a zabukan dake tafe.
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa Isah ya dawo jami’yyar APC daga jami’iyyar NNPP bayan ya ƙasa samun tikitin takarar dan majalisar dokoki a jihar.
Abokin aikin Isah, Murtala Kore wanda ke wakiltar Dambatta ya musanta cewa bai canja sheka daga jami’iyyar APC zuwa Jami’iyyar NNPP ba.
Wasu daga cikin jigajigan jami’yyar APC irin su tsohon gwamna Ibrahim Shekarau sun waske daga jami’yyar APC sun koma Jami’iyyar NNPP duk a cikin wannan mako.