Dalilin da ya sa na ce INEC ba za ta yi sahihin zaɓe a 2023 ba -Odinkalu

Ɗan rajin kare haƙƙin ɗan Adam Chidi Odinkalu ya ce ba lallai ba ne INEC ta shirya sahihin zaɓe a 2023.
Odinkalu wanda tsohon Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin Jama’a ta Ƙasa ne, ya bayyana haka a wata hira da shi a gidan talabijin na Channels TV, a ranar Litinin.
Ya ce “duk da cewa abin murna ne ganin yadda aka samu yawaitar ‘yan Najeriya waɗanda su ka yi rajistar mallakar katin shaidar zaɓe (PVC), samun hukumar zaɓe ta yi adalci shi ya fi mallakar katin muhimmanci.
Odinkalu wanda ƙwararren lauya ne, ya ce bai yi tsammanin INEC a ƙarƙashin shugabancin Muhammadu Buhari za ta yi zaɓe sahihi ba.
“Ni abin da na ke matuƙar takaici shi ne ba lallai ba ne INEC ta yi abin da ya cancanta ta yi ɗin ba. Saboda haka ni dai ina tababar yadda INEC za ta yi sahihin zaɓe a ƙarƙashin wannan gwamnatin. Amma kuma zan bayyana maku dalilai na.”
Ya ce Buhari ya sha cewa zai gudanar da zaɓe sahihi a 2023. Ya ce to wannan kaɗai ya nuna akwai wani a ƙasa.
“Saboda ba aikin sa ba ne gudanar da zaɓe sahihi, saboda INEC hukuma ce mai cin gashin kan ta. To tunda ya na ta nanata cewa zai yi zaɓe sahihi, ya nuna INEC ba ta da ‘yancin cin gashin kan ta kenan.
“A doka INEC ce kaɗai ke da nauyin shirya zaɓe sahihi, ba shugaban ƙasa ba. Babu ruwan sa da yi wa INEC katsalandan. Ita kuma INEC ɗin har yau ba ta ce komai ba kan yadda Buhari ke magana kamar shi ne shugaban hukumar, ya na yi mata uwa-makarɓiya.” Inji Odinkalu, wanda lauya ne kuma Farfesa, sannan marubuci.
Sannan ya nuna damuwa cewa akwai yankuna da dama a ƙasar nan, inda INEC ba za ta iya kai jami’an zaɓe ba a ƙasar nan, saboda matsalar tsaro.
“Ni da ku duk mun sani cewa Gwamna El-Rufai ya rubuta wa Shugaban Ƙasa wasiƙa mai ƙunshe da yadda Boko Haram ɓangaren Ansaru ke riƙe da wasu yankuna a Jihar Kaduna da Neja. Har ma su na yanka wa mazauna yankunan haraji. Hakan na nufin INEC ba za ta iya tura ma’aikatan ta a yi zaɓe a irin waɗannan wuraren ba.” Inji shi.
Odinkalu ya bayyana cewa akwai irin waɗannan yankunan a Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas, waɗanda INEC ba za ta iya kai jami’an ta su gudanar da zaɓuka ba.
“Amma INEC na ta nanata cewa wai za ta shirya zaɓe a dukkan ƙananan hukumomi 774 na faɗin ƙasar nan. Kuma ba gaskiya ba ce.”
Ya ce ya kamata INEC ta fito ta shaida wa duniya inda ba za ta iya shiga ta shirya zaɓuka ba, domin jama’a su tantance tun yanzu.