Dalilin da ya sa gwamnatin Najeriya ta ayyana ‘yan bindiga cewa ‘yan ta’adda ne

Gwamnatin Najeriya ta ayyana wasu gungun ‘yan bindiga biyu da suka addabi Arewa maso Yammacin ƙasar cewa ‘yan ta’adda ne.

An raɗa masu sunan ne tare da duk wasu ƙungiyoyin da ke aikata wasu muggan laifuka masu nasaba da irin hare-haren da su ke kaiwa.

Raɗa wa ‘yan bindiga suna ‘yan ta’adda ya biyo bayan umarnin da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta bayar a cikin watan Nuwamba, 2021 cewa Gwamnati ta ayyana ‘yan bindiga cewa ‘yan ta’adda ne.

Wannan sanarwa ta Gwamnatin Tarayya na cikin wata takarda da Kakakin Yaɗa Labaran Ministan Harkokin Shari’a, mai suna Umar Gwandu ya raba wa manema labarai a ranar Laraba, a Abuja.

“Wannan takarda ta zama shaidar cewa Gwamnatin Tarayya ta ayyana ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda cewa ‘yan ta’adda ne, su da duk wasu ƙungiyoyin da ke aikata ɓarna irin ta su.”

Dama a ranar 29 Ga Nuwamba ne gwamnatin tarayya ta amince za ta ayyana su da suna ‘yan ta’adda, bayan kotu ta bayar da umarni.

An yi ta ƙorafe-ƙorafen neman gwamnati ta ayyana su ‘yan ta”adda, har dai a baya Ministan Tsaro ya fito ya faɗi abin da ya hana Gwamnatin Tarayya ayyana cewa ‘yan bindiga ‘yan ta’adda ne.

A wancan lokacin, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba haka kawai gabagaɗi ake fitowa a ayyana cewa ‘yan bindiga su ma ‘yan ta’adda ne ba.

Ministan Harkokin Tsaro Bashir Magashi ne ya bayyana haka, tare da cewa akwai matakan da ake bi, kuma ko an bi su ɗin, to sai an tabbatar da kammaluwar su sannan za a ayyana cewa ‘yan bindiga ma ‘yan ta’adda ne.

Magashi ya yi wannan furuci a lokacin da ya kai ziyarar gani da idon irin ci gaban da ake samu a filin dagar yaƙi da Boko Haram a Barno.

Ya na tare da rakiyar Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Lucky Iraboh da sauran manyan hafsoshin ƙasa, ruwa da na sama.

Ya kuma gaba da manyan kwamandojin yaƙi na Arewa maso Gabas, wato ‘Threater Commanders’, tare da nuna gamsuwa da irin ƙoƙarin su da nasarorin da ake kan samu a yanzu.

Magashi ya yi wannan bayani ne biyo bayan tambayoyin da manema labarai su ka yi masa a Maiduguri, dangane da tsaikon da ake samu wajen ƙin kiran ‘yan bindiga da suna ‘yan ta’adda da Gwamnatin Tarayya ta ƙi yi.

Cikin makon jiya ne Shehin Malami Ahmad Gumi ya ce “za a yi da-na-sani idan Buhari ya raɗa wa ‘yan bindiga sunan ‘yan ta’adda.”

Babban malamin nan na Kaduna kuma wanda ya riƙa kurɗa-kurɗar shiga wurin ‘yan bindiga, Sheikh Ahmed Gumi, ya gargaɗi Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnatin Tarayya cewa kada su ayyana sunan ‘yan bindiga su ce musu ‘yan ta’adda.

Duk da kashe-kashe da garkuwa da mutanen da ‘yan bindiga ke yi, Gumi ya ce za a yi da-na-sani idan aka yi amfani da dokar ƙasa aka kira su ‘yan ta’adda.

Gumi wanda tsohon soja ne, kuma likita, ya daɗe ya na kamfen ɗin neman a yi wa Fulani ‘yan bindiga afuwa.

Ya shiga wurin ‘yan bindiga a dazukan Kaduna, Neja, Katsina, Sokoto da Zamfara. Kuma ya je jihohin inda ya gana da gwamnoni da gaggan gogarman ‘yan fashin daji masu garkuwa da mutane, da nufin a samu maslahar magance matsalolin da ke addabar yankunan.

Ko kwanan nan Gwamnan Katsina da na Kaduna sun nemi a bayyana ‘yan bindiga cewa ‘yan ta’adda ne, domin sojoji su samu cikakkiyar damar murƙushe su.

Sai dai Gumi a cikin wani bayani da ya wallafa a shafin sa na Facebook, ya yi babban kuskure ne idan aka bayyana ‘yan bindiga cewa ‘yan ta’adda ne.

Duk da ya nuna cewa su ma ‘yan bindiga su na kisa da ɓarnatar da dukiyar jama’a da garkuwa da mutane, to amma siyasa ta shiga cikin zukatan jama’a, musamman masu cewa su ma ‘yan bindiga ai ‘yan ta’adda ne.

Ya yi tsokaci kan yadda ‘yan bijilante ke kashe Fulanin da ba su ji ba, ba su gani ba, su ce duk ‘yan bindiga ne, abin da Gumi ya ce hakan kan tunzira sauran su shiga ƙauyuka kisan ramuwar-gayya.

Gumi ya bayyana irin ƙoƙarin da ya yi har ya sa wasu Fulani ‘yan bindiga masu yawa su ka tuba, su ka daina.

“Sai dai abin takaici, ba ni da masu taya ni wannan mawuyacin aiki da nake yi, maimakon haka ma, sai tulin masu gaba da ni na ke ƙara samu a kullum.”

Ya yi fatan a samu wani limamin Kirista na Igbo da ka Yarabawa su je su lallashi Nnamdi Kanu da su Sunday Igboho masu son ɓallewa daga Najeriya.

Ya ce idan su ka wayar wa magoya bayan su kai, za a samu maslahar zamantakewa tare da juna a matsayin mu na ƙabila daban-daban masu zaune a ƙasa ɗaya.

Ya ce malaman addini za su iya taka muhimmiyar rawa inda tsarin da babu addini ba zai iya yin tasiri ba.

Sai dai ya nuna takaicin maimakon jama’a su tashi tsaye a kwantar da wannan mummunar fitina, sai kowa ya yi zaman sa cikin ɗaki. Ya dararrashe ya na ta watsa bayanai barkatai waɗanda ba za su taɓa zama mabuɗin kawo ƙarshen fitintinu ba.

A ranar Lahadi ce dai Buhari ya bayyana cewa ‘yan bindiga da ba su da bambanci da Boko Haram.

Duk da dai har yau Shugaba Buhari bai fito ya bayyana ‘yan bindiga cewa su ma ‘yan ta’adda ne kamar yadda ake kiran ‘yan Boko Haram ba, a ranar Lahadi ya bayyana cewa “a wani ɓangaren ‘yan bindiga ba su da wani bambanci da ‘yan Boko Haram.”

Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaba Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka, a ranar Lahadi, bayan da wata mujalla mai suna The Economist, wadda ake bugawa a Landan ta buga labari cewa rashin tsaro a Najeriya ya ƙara dagulewa a ƙarƙashin mulkin Buhari.

‘Yan bindigar dai yanzu sun yi ƙarfin da har sun kai ga harbo jirgin yaƙin Najeriya ɗaya. Waɗanda Shehu ya ce sun yi ƙarfin tara kuɗaɗe da muggan makamai. “Kenan a nan ba su da wani bambanci ma da Boko Haram, waɗanda su a yanzu ma an yi masu tara-tara, an matse su a wuri ɗaya.”

‘Yan Najeriya da dama ciki har da Majalisar Dattawa da Gwamna El-Rufai na Kaduna, duk sun yi kira ga Buhari ya kira ‘yan bindiga cewa ‘yan ta’adda ne.

A martanin da Shehu ya yi masu, ya amince akwai ƙalubale daban-daban kan matsalolin tsaro a sassan ƙasar nan daban-daban.

Sai dai kuma ya ce duk Shugaba Buhari ya na ta ƙoƙarin magance matsalolin.

“Mujallar The Economist ta yi gaskiya, Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro da dama. Sai dai a lura ba a cikin wannan gwamnatin matsalolin su ka faru ba. Wannan gwamnatin ce ma ke ta ƙoƙarin magance waɗannan ɗimbin matsalolin. “Alhali gwamnatocin baya babu wadda ta yi ƙoƙarin magance ko da matsala guda tal.” Inji Garba Shehu, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, kuma ya aiko wa PREMIUM TIMES.

Ko a cikin makon da ya gabata, sai da Gwamna El-Rufai ya goyi bayan Majalisar Dattawa Tarayya domin kiran ‘yan bindiga da suna ‘yan ta’adda.

Gwamna Nasiru El-Rufai na Jihar Kaduna ya bayyana goyon bayan sa ga Majalisar Tarayya, wadda ta yi kira ga Gwmnatin Tarayya cewa ta shaida wa duniya ‘yan bindiga su ma ‘yan ta’adda ne kawai.

El-Rufai ya ce idan aka bayyana cewa ‘yan bindiga su ma ‘yan ta’adda ne, to hakan zai ƙara zaburar da sojoji su darkake su a duk inda su ke, su na yi masu kisan kan-mai-uwa-da-wabi, ba tare da tsoron ƙorafe-ƙorafe daga bakunan ƙungiyi kare haƙƙi na kasashen duniya ba.